Rundunar sojin saman juyin juya halin Musulunci ta Iran ta bayyana jirgin sama marar matukin mai dauke da tarun makamai wadda kan iya kai hare-hare a kan abubuwa har guda 9 shi kadai.
Jirgin yana da fadin fukafukai kimanin mita 22 yana kuma tashin kimanin kilomita 3,100.
Yana kuma yin awa 35 yana gudun a sararin samaniya, sannan kuma ya kanyi tafiyar kilomita 350 a cikin awa 1.
Jirgin yana iya daukar abu mai nauyin kilograms 500 hakan kan bashi damar daukar boma-bomai guda 13, yan da range kilomita 1000, zai yi nisan kilomita 4000 daga gurin wadda ke kula da shi.
Jirgin an gwada shi a Lahadi nan da ta gabata a yayin rawar dajin da Iran din tayi, ya kuma farfasa abubuwa kimanin 8 lokaci guda.
U Akbar Kiyawa