Tare da girmamawa muke godiya ga Al'ummar musulmi na gida da wajen kasarnan da duniya baki daya da suke mana fatan alkhairi da adduoi na musamman don ganin anyi nasarar kawar da wannan gubar ta'addanci dasu Bello Turji suka haddasa mana, cikin wannan fatar harda labarin sako mutanenmu da azzalumi Turji yake rike dasu.
Kawo yanzu da nake rubutunnan, munada mutane daga karamar hukumar Shinkafi sun kai sittin mutun sittin (60) hannun Bello Turji suna jiran akai kuɗɗi a karbosu, mutanen da aka sako yau kuddin fansa aka kai aka karbosu.
A Birnin Yero kaɗai akwai mutum ashirin da bakwai (27) a hannunsu, Shanawa akwai mutum goma sha biyar, (15) kayaye mutum tara (09) Shinkafi akwai mutum yakai biyar (05), Badarawa ma akwai mutum yakai shidda (06), Ina tunanin ba'a mutunta kamammin ba da "yan'uwansu da waɗanda aka fanso idan ba'a sanar da duniya halin da suke ciki ba.
Ku cigaba da tanyamu adduah Allah madaukakin sarki Ya tarwatsa wadanan azzalumai da masu taimakonsu ta kowace hanya. Allah Yasa karshensu yazo Amin.