TALKAFIN AMURKA GA SOJOJIN LEBANON DOMIN KARA HANA SOJOJIN NA LEBANON RAWAR GABAN HANTSI,

 Tallafin Amurka ga sojojin Lebanon



Domin ƙara hana sojojin na Lebanon rawar gaban hantsinsu, Amurka, wadda Hezbollah ke gani a matsayin babbar maƙiyarta, ita ce kan gaba wajen tallafa wa sojojin Lebanon. A wasu ƴan lokuta ma Amurkar ce ke taimakawa wajen biyan albashin sojojin na Lebanon.


Sai dai sun fi bayar da tallafin motoci da kayan kariya da wasu makamai waɗanda ba su kai girman irin waɗanda take ba Isra'ila ba.


Sai dai wasu na ganin rashin kataɓus ɗin sojojin Lebanon a kan Isra'ila ba a kan ƙasar kaɗai ya tsaya ba.


"Ba rundunar sojin Lebanon ba, babu wata rundunar sojin ƙasashen Larabawa da za ta iya fuskantar rundunar sojin Isra'ila," in ji Janar Mounir Shehade, tsohon kodinetan gwamnatin Lebanon a dakarun Majalisar Ɗinkin Duniya a Lebanon wato Unifil.


"Idan za ka gwabza da Isra'ila, sai dai ka yi amfani da fasahar yaƙin sari ka noƙe kamar yadda ake yi a Gaza."


Sojojin Lebanon suna gadin ƙofar shiga wani asibiti a Beirut a ranar 17 ga Satumban 2024 (AFP via Getty Images)Asalin hoton,Getty Images

Bayanan hoto,Sojojin Lebanon suna gadin ƙofar shiga wani asibiti a Beirut a ranar da na'urori suka fashe suka kashe gomman mutane, sannan suka jikkata dubbai.

Khalil El Helou, wani tsohon janar ne a rundunar sojin Lebanon, ya ce, "aikin sojojin Lebanon shi ne samar da daidaito da kwanciyar hankali a cikin ƙasar. Yadda yaƙin ya tursasa magoya bayan Hezbollah kusan rabin miliyan zuwa yankunan da ba sa ƙaunar Hezbollah ya haifar da zaune-tsaye wanda zai iya jawo rikici har ma ya iya kai ga yaƙin basasa a ƙasar," in ji shi.


Bayan kashe jagoran Hezbollah, Hassan Nasrallah da Isra'ila ta yi, an tura sojojin Lebanon zuwa yankunan da ake tunanin za a samun rikicin tsakanin ɓangarorin a ƙasar.


Ta kuma fitar da sanarwa a ranar Lahadin da ta gabata, inda take kira ga "ƴan ƙasar su tabbatar da haɗin kan ƙasa."

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post