Mbappe ba zai buga wa Faransa Nations League ba
Kylian Mbappe ba zai buga wa Faransa Nations League ba, duk da ya murmure daga raunin da ya yi jinya.
Bai yiwa Real Madrid wasan da ta tashi 1-1 ba da Atletico Madrid ranar Lahadi, amma ya buga karawar da Lille ta ci Real 1-0 a Champions League ranar Laraba.
Duk da ya buga wa Real Madrid gasar zakarun Turai, amma Didier Deschamps bai gayyace shi wasan da zai fuskanci Israel da Belgium ba.
Mbappe ya ci ƙwallo bakwai a wasa 10 tun bayan da ya koma Real Madrid a bana daga Paris St Germain.
Haka shima Antoine Griezmann ba zai buga karawar ba a karon farko, wanda ya sanar da yin ritaya ranar Litinin.
Mai shekara 33 ya buga wa Faransa wasa 137 da lashe kofin duniya a Rasha a 2018 da kai wa wasan karshe a Qatar a 2022.
Christopher Nkunku, wanda ya buga wa Faransa wasa na 10 a watan Yuni, yana cikin waɗanda aka gayyata, amma banda N'Golo Kante.
Faransa za ta fara ziyartar Israel ranar Alhamis 10 ga watan Oktoba a Budapest daga nan ta kece raini da Belgium a Brussels ranar Litinin 14 ga watan Oktoba.
Kawo yanzu Faransa tana ta biyu a rukuni na biyu a League A da maki uku, bayan wasa biyu, yayin da Italiya ke jan ragama mai maki shida.
Ƴan wasan da Faransa ta gayyata:
Masu tsaron raga: Alphonse Areola (West Ham United), Mike Maignan (AC Milan), Brice Samba (Lens)
Masu tsaron baya: Jonathan Clauss (Nice), Lucas Digne (Aston Villa), Wesley Fofana (Chelsea), Theo Hernandez (AC Milan), Ibrahima Konate (Liverpool), Jules Kounde (Barcelona), William Saliba (Arsenal), Dayot Upamecano (Bayern Munich)
Masu buga tsakiya: Eduardo Camavinga (Real Madrid), Youssouf Fofana (AC Milan), Matteo Guendouzi (Lazio), Manu Kone (Roma), Aurelien Tchouameni (Real Madrid), Warren Zaire-Emery (Paris St-Germain)
Masu cin ƙwallaye: Bradley Barcola, Ousmane Dembele, Randal Kolo Muani (all Paris Saint-Germain), Christopher Nkunku (Chelsea), Michael Olise (Bayern Munich), Marcus Thuram (Inter Milan)