ISRA'ILA TA SAKE RUWAN BAMA-BAMAI A BEIRUT

 Isra'ila ta sake ruwan bama-bamai a Beirut



Isra'ila ta sake ruwan bama-bamai a babban birnin Lebanon, Beirut, inda rahotanni ke cewa shugaban kungiyar Hezbollah na gaba na daga cikin wadanda ta hara.


Kafofin yada labarai na kasar sun bayar da rahotannin akalla hari goma da Isra'ilar ta kai ciki har da daya da ta kai a kusa da wajen babban filin jirgin saman birnin ranar Alhamis wayewar Juma'a.


Duk da cewa babu tabbaci to amma alamu na nuna cewa ruwam bama-baman da Isra'ilar ta yi a cikin daren tana harin shugabannin kungiyar Hezbollah ne.


Rahotanni sun ce hare-haren sun yi kama da wadanda ta kai ta hallaka shugaban kungiyar Hassan Nasrallah a makon da ya gabata.


Yankunan da ta kai hare-haren sun hada da Dahieh – wanda wuri ne da kungiyar ke da karfi a babban birnin na Lebanon, Beirut


Ana iya ganin yadda hayaki ke ta tashi a birnin yayin da safiyar Juma’a ke wayewa.Wasu rahotanni da ke ambato jami'an Isra’ila na cewa an kai hare-haren ne da nufin hallaka shugabannin kungiyar musamman ma mutumin da ake ganin shi ne zai kasance shugabanta na gaba Hashem Safieddine, wanda abokan wasa ne da marigayi Nasrallah.


Wasu bayanai na nuna cewa mutumin na boye a wani wuri mai sulke na karkashin kasa, to amma ba a san takamaimai halin da yake ciki ba.


Can a wani bangaren na daban kuma hukumomin sojin Lebanon sun ce an kashe musu sojinsu biyu a kudancin kasar, yayin da dakarun Isra'ila ke kutse da dannawa ta kasa don kawar da mayakan Hezbollah, tare da bayar da umarni ga mazauna garuruwa da kauyuka 20 da ke wannan bangare na kudancin Lebanon su tashi, domin abin da Isra'ilar ta ce kare lafiyarsu.


Sojojin Isra'ila ba su ce komai ba dangane da batun kisan sojin na Lebanon, illa dai sun ce dakarunsu sun kashe mayakan Hezbollah a kusa da iyaka.


Ita ma Hezbollah ta ce ta hari dakarun na Isra’ila a dukkanin bangarorin biyu


Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce an dan jikkata ma’aikatanta na sa-kai biyu, kuma ana tsara inda za su je ne tare da dakarun wanzar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post