Batun wa'adin shugaban ƙasa na janyo ce-ce-ku-ce a Najeriya

 Batun wa'adin shugaban ƙasa na janyo ce-ce-ku-ce a Najeriya



Ana ci gaba da sharhi da bayyana mabanbantan ra’ayoyi a kan buƙatar da tsohon mataimakin shugaban Najeriya ya gabatar wa majalisar dattawa game da yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar gyaran fuska.


Atiku Abubakar wanda ya yi wa jam’iyyar PDP takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 ya nemi kwamitin majalisar dattawan wanda ya fara aikin gyaran kundin tsarin mulki na1999, a wata takardar neman a gyara wa’adin shekarun shugaban ƙasa zuwa wa'adi ɗaya na shekara shida.


Wannan buƙata ta tsohon mataimakin shugaban ƙasar ta zo ne a daidai lokacin da ake shirye-shiryen yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar gyaran fuska, kuma jama'a da masana da ƙungiyoyi ke ta bayyana abubuwan da suke ganin ya kamata a gyara a kundin.


Baya ga shawarar da ya bayar kan wa'adin shugaban ƙasar, Atiku Abubakar ya buƙaci a mayar da mulkin ƙasar ya zama na karɓa-karɓa tsakanin yankunan ƙasar guda shida,


Ƴan siyasa da masana sun fara tsokaci kan shawarar tsohon mataimakin shugaban ƙasar, inda wasu kamar su Hon. Farouk Jarma na jami'yyar PDP ke ganin wannan shawarar ita ta fi dacewa da siyasar Najeriya.


''Wannan shawarar da Wazirin Adamawa ya bayar na kowace shiya ta sami damar fitar da shugaban ƙasa, idan aka yi haka za a sami haɗin kai kuma rashin jituwa da ake fama da shi zai ragu, za a kawar da bambancin addini da na ƙabila kuma hakan zai kawo cigaban ƙasa.'' In ji shi


Hon. Farouk ya kuma ƙara da cewa rashin yin hakan zai hana wasu yankunan ƙasar damar iya fitar da shugaban ƙasa daga yankinsu, inda ya ce hakan na iya zama rashin adalci a garesu.


Ya ce: ''Yin shekara shida zai bai wa kowane shugaban ƙasa da aka zaɓa damar gudanar da duk ayyukan da suka kamata kafin ƙarshen wa'adinsa, inda wata shiya kuma za ta kawo nata.''

A wani ɓangaren kuma akwai waɗanda ke ganin mayar da wa'adin shugaban ƙasa ya zama guda ɗaya na shekara shida zai iya haifar da halin ko-in-kula a zukatan shugabannin.


Kamar yadda Garba Kore Dawakin Kudu, wani jigo a jami'yyar APC ya yi wa BBC bayani, inda ya ce: ''Halin mutum jarinsa, duk lokacin da ka zama shugaba mai wa'adin shekara huɗu dole za ka yi alkhairi a cikin waɗannan shekara huɗun domin kana son ka koma kan mulki, amma a halin ɗan Najeriya, idan ya tabbatar cewa mulki sau ɗaya zai yi, tabbas ba zai raga wa kowa ba kuma ba zai ji kunyar kowa ba, zai yi ɓarna yadda yake so ya kuma ɓata da kowa yadda yake so.''


Garba Kore Dawakin Kudu ya ƙara da cewa yadda wa'adin shugaban ƙasar yake a yanzu shi ne ya fi dacewa da dimokuraɗiyya domin hakan ne zai tabbatar da cewa shugabanni za su yi wa talakawa aiki.


Rahotanni dai na cewa tuni kwamitin gyaran kundin tsarin mulkin Najeriyar na majalisar dattawan ƙasar ya fara zama domin tattara bahasi da bayanen ƴan Najeriya wanda ake fatan za a gabatar a gaban majalisa kafin ɗaukar mataki na gaba.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post