AN SAMO KARIN GAWAR MUTUM BIYU DAGA WADANDA KWALE-KWALE YA KIFE DA SU A JIHAR NAIJA.

 An samo ƙarin gawar mutum biyu daga waɗanda kwale-kwale ya kife da su a jihar Naija



Hukumar agajin gaggawa ta jihar Naija, ta ce da safiyar ranar Alhamis jami'an da ke aikin ceto mutanen da kwale-kwale ya kife da su ranar Talata sun ƙara samo gawar mutum biyu.


Mai magana da yawun hukumar, Ibrahim Audu Hussaini ya shaida cewa "kawo yanzu an samu gawar mutum 18 tun fara aikin. Sannan kuma an ceto mutum 150 da ransu."


Sai dai kuma kakakin hukumar bai faɗi ragowar mutanen da ake nema ba amma ya ce " ana sa ran sun wuce mutun 100."


A ranar Talata ne dai kwale-kwalen ya kia cikin kwale-kwalen lokacin da ya kife a madatsar ruwa ta Jebba a garin Gbajibo da ke ƙaramar hukumar da yammacin ranar 


Kwale-kwalen wanda ya taso daga Mundi zai tafi Gbajibo domin halartar bikin Maulidi cike yake maƙil da mata da ƙananan yara.


Har yanzu dai ana ci gaba da gudanar da ayyukan ceto ƙarƙashin jagorancin hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar da sauran mutane.


Ko a watan Satumban 2023, an samu kwatankwacin irin wannan, inda kwale-kwale ɗauke da fasinja 50 ya kife kuma ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 24 a jihar.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post