Saka zai buga wa Arsenal Champions League da Atalanta
Bukayo Saka zai buga wa Arsenal Champions League da za ta je Atalanta ranar Alhamis a kokarin da Mikel Arteta ke fatan taka rawar gani a bana.
An sauya Saka a wasan hamayya da Arsenal ta je ta doke Tottenham 1-0 a Premier League ranar Lahadi.
Tuni aka sanar da cewar ƙyaftin Martin Odegaard yana jinya, wanda bai buga wasan Tottenham ba, to sai dai Declan Rice zai yi karawar.
Rice bai yi wasan Premier League ranar Lahadi ba, sakamakon hukuncin jan kati da aka yi masa a wasan da aka raba maki tsakanin Arsenal da Brighton a Premier League.
Haka shi ma mai tsaron bayan tawagar Italiya, Riccardo Calafiori ya murmure, bayan jinya, watakila ya buga wasan farko da Gunners za ta yi a babbar gasar tamaula ta zakarun Turai ta kakar nan.
An yi waje da Arsenal a kwata fainal a Champions League a bara a hannun Bayern Munich.
Sakamakon wasannin Champions League da aka buga ranar Laraba:
Bologna 0 - 0 Shakhtar Donetsk
Sparta Prague 3 - 0 Red Bull Salzburg
Celtic 5 - 1 Slovan Bratislava
Club Brugge 0 - 3 Borussia Dortmund
Manchester City 0 - 0 Inter Milan
PSG 1- 0 Girona
@Ma'asumah Nigerian News update