ISRA'ILA TA KASHE AHUGABAN HEZBOLLAH SAYYED HASSAN NARULLAH

 Isra'ila ta kashe shugaban Hezbollah Hassan Nasrallah 



Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kashe shugahan ƙungiyar Hezbollah, Hassan Nasrallah.


Cikin wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na X, ta ce ''Daga yanzu Hassan Nasrallah ba zai sake yi wa duniya ta'addanci ba''.


Kisan nasa na zuwa ne bayan jerin hare-hare cikin dare da Isra'ila ta riƙa kai wa birnin Beirut, da ta ce tana kai wa Nasrallah da sauran kwamandojin ƙungiyar Hezbolla.


Sanarwar ta ci gaba da cewa, bayan Hassan Nasarallah, an kuma kashe wasu manyan kwamandojin ƙungiyar da ke samun goyon bayan Iran, ciki har da babban kwamandanta mai lura da kudancin Beirut.


Sojojin na Isra'ila sun ce wani jirgin yaƙinsu ne ya kai hari tsakiyar shalkwatar Hezbollah, wanda suka ce yana ƙarƙashin ƙasa a ƙasan wani gida da ke unguwar Dahieh a birnin Beirut.


Sanarwar ta ƙara da cewa an kai harin ne, yayin da ''manyan kwamandojin'' ƙungiyar ke gudanar da harkokinsu a wajen unguwar Dahieh da ke kudancin birnin Beirut, wanda yanki ne da ƙungiyar Hezbollah ke da ƙarfi.


A nata ɓangare, ƙungiyar Hezbollah ta tabbatar da kisan jagoran nata.


Cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Telegram ta ce ''za ta ci gaba da yaƙi da Isra'ila da goyon bayan Gaza da Falasɗinawa tare da kare Lebanon da mutanenta''.

Wane ne Sheikh Hassan Nasrallah?

Tun shekarar 1992 fitaccen malamin addinin musulunci mabiyin darikar Shi'a, Sheikh Hassan Nasrallah ke jagorantar ƙungiyar Hezbollah.


Ya taka muhimmiyar rawa wajen sauya ƙungiyar zuwa ta siyasa, da inganta sojinta da mayaƙa.


Sheikh Nasarallah na da alaƙar ta kusa da jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei.


Hakan ya samo asali tun shekarar 1981, a lokacin da jagoran addinin musulunci na farko a Iran Ayatollah Ruhollah Khomeini, ya naɗa shi muƙamin mataimaki na musamman a Lebanon.


Shekaru da dama ba a ga Nasrallah a bainar jama'a ba, watakila saboda fargabar Isra'ila na iya kashe shi, to sai dai a baya-bayan nan ya riƙa bayyana tare da yi wa mabiyansa jawabi, musamman kan hare-haren Isra'ila a Gaza da Hezbollah.


Ko a makon da ya gabata ma Sheikh Nasaralla ya yi wa magoya bayansa jawabi a Beirut in da ya ce babu wani abu da Isra'ila za ta yi da zai sa su daina kai mata hari yankin arewaci inda Yahudawa 'yan kama wuri zauna suke.


Ya gabatar da jawabin ne a matsayin martani bayan hare-haren da ƙungiyarsa ke zargin Isra'ila ta kai ta na'urorin sadarwa da Hezbollah ke amfani da su a Lebanon.


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post