Hezbollah ta zargi Isra'ila da kai hari ta na'ura da ya jikkata dubbai a Lebanon

 Hezbollah ta zargi Isra'ila da kai hari ta na'ura da ya jikkata dubbai a Lebanon



Ma’aikatar harkokin wajen Birtaniya ta bi sahun Majalisar Dinkin Duniya da Amurka wajen kira da a kai zuciya nesa bayan da wasu kananan na’urori da kungiyar Hezbollah ke amfani da su wajen sadarwa suka faffashe a lokaci guda a fadin Lebanon a ranar Talata a abin da ake gani kamar wani hari ne tsararre.


Akalla mutum tara ne suka mutu wasu kusan 3000 suka ji rauni a harin wanda kungiyar ta dora alhakinsa kan Isra’ila, tare da lasar takobin cewa za ta rama.


Babu dai wata sanarwa a hukumance daga Isra'ila kan lamarin.


Tuni daman kafin wannan harin ana cike da fargaba da barkewar sabon rikici tsakanin Isra’ila da kungiyar ta Hezbollah a Lebanon.


Shugabannin Isra’ila na ta barazanar kara ayyukansu na soji domin mayar da dubban ‘yan Isra’ila da suka tasa daga arewacin kasar bayan kusan shekara daya ta musayar wuta da ake yi a kan iyaka, wadda yakin Gaza ya haifar.


Sai kuma ga shi yanzu Hezbollah ta yi barazanar daukar fansa kan wannan sabon babban hari da aka kai mata.


Asibitoci a Lebanon sun cika da mutanen da harin ya shafa, bayan da na’urorin suka farfashe.


‘Yan Lebanon da dama sun kasance cikin yanayi na dimuwa da mamaki a lokacin da abin ya faru, sun kasa fahimtar yadda abin ya faru, kasancewar ba su taba ganin irinsa ba a girma da kuma yanayinsa.


Hezbollah ta ce an yi kutse a wadannan kananan na’urorin sadarwa da ba ta ambaci yawansu ba – da ta dogara da su sosai wajen sadarwa saboda yuwuwar satar sauraro da ganin bayanan wayar salula, inda suka farfashe a babban birnin kasar Beirut da sauran wurare da dama.


An ga wani hoton bidiyo da ke nuna fashewar a jakar wani mutum ko aljihunsa a wani babban kanti. Daga nan sai aka ga mutumin ya fadi baya yana kumaji, jama’a suna ta guduwa.


Har bayan wasu sa’o’i ana ji da ganin motocin asibiti na ta kai komo zuwa asibitocin da suka cika da wadanda abin ya rutsa da su.


Ministan lafiya na kasar, ya ce mutum 200 daga cikinsu suna cikin mawuyacin hali.


Ana iya ganin ‘yan uwa da dangin wadanda suka jikkata a kofar asibitoci don sanin halin da ‘yan uwan nasu ke ciki.


Yawancin raunukan da mutanen suka ji a kugu ne da fuska da ido da hannu, wasu mutanen da dama sun rasa yatsunsu in ji ministan.


Matar jakadan Iran a Lebanon ta ce , mijinta ya dan ji rauni shi ma a harin.


Ofishin yada labarai na kungiyar Hezbolah ya sanar da mutuwar mayakan kungiyar takwas a harin, amma kuma bai bayar da karin bayani ba, illa dai cewa sun yi shahada a kan hanyarsu ta zuwa Birnin Kudus.


Can ma a Syria, inda mayakan Hezbolah ke yaki tare da dakarun gwamnati, an bayar da rahoton cewa mutum 14 sun ji rauni a irin wannan fashewa ta karamar na’urar.


Duk da cewa hukumomin sojin Isra’ila sun ki cewa komai a kan wannan hari, kafofin yada labarai na duniya na ruwaito wasu kafofin sojin Amurka da kafofin Lebanon wadanda duka ba su bayyana sunansu ba, na cewa jami’an sirri na Isra’ila sun boye wasu ‘yan abubuwa masu fashewa a cikin wannan ‘yan kananan na’urorin sadarwa da aka shigar Lebanon, kuma ‘yan Hezbollah suke amfani da su.


Mataimakiyar darekta a shirin tsaro na kasa da kasa a Cibiyar nazarin kasa da kasa da dabaru da ke Washington a Amurka - (Centre for Strategic da International Studies), Emily Harding, ta gaya wa BBC abin da ya faru da kuma yadda take ganin zai iya shafar ayyukan Hezbollah.


Ta ce : ''Abin zai yi tasiri sosai, wajen kudurinsu, sannan zai haifar da nakasu ga ayyukansu matuka. A bangaren kuduri, za su rinka tababa ko tsananta bincike a kan dukkanin abin da ya shafi tsaronsu a yanzu, za su yi mamakin wane ne a cikin wadanda ke da hannu wajen sama musu na’urar ya ci amanarsu, za su rika bincike a kan dukkanin hanyoyin sadarwarsu.’’

@Ma'asumah Nigerian News update

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post