Basaraken Zamfara da ya yi wata bakwai bayan karɓar kuɗin fansa ba a sako shi ba'
Ƴan bindigaAsalin hoton,NPF
Mazauna garin Zarumai da ke ƙaramar hukumar Bukkuyum a jihar Zamfara, sun yi kira ga hukumomi da su taimaka wajen ganin an sako basaraken yankin da ƴan bindiga suka yi garkuwa da shi na tsawon lokaci.
Iyalan uban ƙasar na Zarumai sun koka da yadda ƴan bindiga suka karɓi kuɗin fansa kuma suka ƙi sako basaraken da suke riƙe da shi tare da wasu mutane guda biyu.
A cewar Aminu Ibrahim wanda ɗa ne ga Uban ƙasar har yanzu suna magana da ƴan bindigar da kuma waɗanda aka yi garkuwa da su wanda suka shafe sama da wata bakwai suna hannun ƴan bindigar bayan kuma sun karɓi kuɗin fansa da ya kai sama da Naira miliyan 15.
‘’Bayan mun biya su kuɗin fansar, sai suka ƙi sako shi inda suka ce sai mun kai masu babura guda 5 da ƙarin Naira miliyan 5, kuma ba mu da kuɗin nan domin duk wasu kadarori da muke da su mun sayar a halin yanzu.’’ In ji shi
Ya ƙara da cewa a duk lokacin da suka yi magana da mahaifin nasu babu abin da ya ke nanatawa sai dai buƙatar ya ga cewa an kuɓutar da shi.
Ya ce: ‘’Yanzu babu wata hanya da za mu bi sai dai ta addu’a saboda ba kuɗin ne muke da su ba, kuma saboda halin da ake ciki na matsin rayuwa ba kowa ne ke iya taimakawa ba. Duk wanda za ka je wurin shi neman taimako shi ma ta kanshi yake yi.’’
Ya buƙaci hukumomin jihar da su taimaka a yunƙurin da ake yi na kuɓutar da basaraken.
@Ma'asumah Nigerian News update