BAMU DA FARGABAR AMBALIYAN RUWA ZA TA SHAFI MADATSAN TIGA DA CHALAWA GOBE

 Ba mu da fargabar ambaliyar ruwa za ta shafi madatsun Tiga da Challawa Gobe'



A Najeriya hukumar raya kogunan Hadejia Jama’are ta tabbatar da cewa madatsun ruwan Tiga da Challawa Goje a jihar Kano lafiya kalau suke.


Hukumar ta ce tawagar kwararrun ma’aikatanta ta ziyarci madatsun ruwan don duba halin da suke ciki, sakamakon korafe-korafen da aka samu bayan mummunar ambaliyar ruwan da ta auku a jihar Borno.


Babban manajan daraktan hukumar Ma’amun Da’u Aliyu, ya shaida wa BBC cewa babu wata fargaba da suke da ita musamman ta ambaliyar ruwa.


Malam Da'u ya ce damuwar da mutane suka nuna na daga cikin dalilin da suka gayyaci kwararru domin zuwa madatsun ruwan da yin kwakkwaran binciken tabbatar da ingancinsu.



''Ruwan da ke cikin madatsar ruwa ta Tiga, ya ninka wanda ke Alau sau goma sha biyar, shi ya sa muka debi injiniyoyinmu da ke hedikwata, da injiniyoyin da ke Tiga muka zagaya tare, muna da tabbacin dam din nan lafiya yake babu wata matsala, kama tun daga farko da inda a ka yi masa katanga, da jingar da ta tare ruwan komai lafiya lau babu wata matsala.''


Malam Da'u ya ce duk wani abu da ya dace a yi wa madatsar ruwa ana kokarin yin hakan a madatsun Challawa goje, da Tiga, yawancin abin da ke kawo haurowar ruwan har ya yi ambaliya yana da nasaba da rashin gyarawa da kwashewa, to amma a nasu bangaren ana amfani da ruwan domin noman rani.


Nigeria: Yadda za a kauce wa ambaliyar ruwa

1 Agusta 2017

Ambaliya ta yi barna a jihar Gombe

3 Satumba 2015

Yadda kogin Tiga ya haddasa ambaliyar ruwa a wasu yankunan Kano

12 Satumba 2022

''Ita madatsar ruwa ba a yashe ta, musamman mai girma irin wannan. Daman ana yashe madatsar ne idan ta cike to mu kuma a namu bangaren, saboda daukar matakan da suka hada da bude ruwan ya gangara domin noman rani ko ya tafi kogi, saboda duk dattin da ke ciki da zarar an bude shi zai tafi da dattin nan.


Muna hana mutane yin noma a kwaryar madatsar ruwa, saboda noma irin wannan ba bisa ka'ida ba na kara antaya kasa ta cika kogi daga nan ta sake komawa matsadar ruwan.


Akwai na'urori da a kowacce rana suke nuna mana halin da madatsar ruwan ke ciki, akwai wadanda ke kula da shigar ruwan da fitarsa, ana yin komai kan tsarin kimiyya ana kuma adana sakamakon abin da aka samu.''


Ya kara da cewa ba su da wata fargaba kan madatsun ruwan Challawa Goje da Tiga, daman kogunan da ke sako ruwa su shigo nan bangaren na tsaunukan jihar Filato da ke arewa ta tsakiyar Najeriya ne, kuma har a wannan lokacin na damuna ruwan da ke shiga bai taka kara ya karya ba. Hukumomin sun ce suna sa ran bana dam din Tiga da Challawa Goje ba za su yi cikar da za su janyo ambaliyar ruwa ba.


''A yanzu dai batun ambaliyar ruwa daga madatsar ruwa ta Challawa Goje ko Tiga babu ita, in sha Allahu,'' in ji Malam Da'u.


Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da aikin ceton wadanda ambaliyar ruwa ta ritsa da su a birnin Maidugurin jihar Borno sanadiyyar ballewar da madatsar ruwa ta Alau ta yi.


Kusan mutane miliyan biyu ambaliyar ta shafa kamar yadda Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya shaida wa BBC, kuma ya yi wuri a iya tantance yawan asarar dukiya da gidaje da gonaki, da makarantu da asibitoci da sauransu, da ambaliyar ta daidaita a jihar.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post