AN ZAKULO GANGAR JIKIN SAYYED HASSAN NARULLAH DAGA BARAGUZAI



An zaƙulo gawar Hassan Nasrallah daga ɓaraguzai

Bayanan hoto,Wasu magoya bayan Hassan Nasrallah kenan suke alhinin mutuwarsa a Lebanon

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ba da rahoton cewa an zaƙulo gawar shugaban Hezbollah Hassan Nasrallah daga wurin harin da ya yi ajalinsa a kudancin birnin Beirut na Lebanon.


Wasu majiyoyi daga asibiti da kuma na tsaro sun shaida wa Reuters cewa gawar "ba ta ɗauke da wani rauni".


A jiya Asabar ne Hezbollah ta tabbatar da mutuwarsa bayan harin da aka kai da tsakar dare a ranar Juma'a.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post