Ya ce : Auren mut'ah ba aure bane auren banza ne , auren jeka nayika ne kuma ba auren Allah da Annabi bane , a lokaci guda kuma yace Annabi (saww) ya taɓa halasta auren mut'ah a farkon Musulunci .
Abun tambaya zai yu Annabi (saww) ya halastawa mutane wani ƙazamin aiki da sunan aure tunda dai ba aure bane ?
Ya ce : Auren mut'ah ba aure bane saboda ba a gado a cikin sa tsakanin mata da miji , idan akwai sadaki akwai aure idan babu sadaki babu aure .
Shin basu bane suka ce ba a gadon Annabawa ciki har da Annabinmu (saww) !
Abun tambaya idan gado shine sharaɗin ingancin aure ya zai yi da auren Annabi (saww) bayan sunce ba a gadon Annabawa ?
Ko dai ya yarda gado ba sharaɗi bane na aure ya ƙaryata kansa ko kuma ya yarda ya taɓa kimar auren shugaba (saww) ko kuma ya yarda ana iya aure ba gado kamar auren mut'ah bashi da zaɓi na uku anan .
✍️Khadimul Ashrãf Al-Abdul Faneey Al-kanaweey.