WATA GASKIYA MAI ƊACI DA WASU SUKA KASA FAHIMTARTA

 WATA GASKIYA MAI ƊACI DA WASU SUKA KASA FAHIMTARTA  



1 . Duk mai hankali da tunani yasan tunda har Malam Zakzakiy (H) ya fito ya faɗa yace ga wanda nake Taƙildi da shi kuma ga yanda mas'alar taƙlidi take to tun anan ya bayyanawa mabiya cewa baya buƙatar dole sai mutum yayi duk irin abinda yake yi a duk mas'alolin Addini ko ya yi daidai da shi a cikin duk wani ra'ayi na Addini babba da ƙarami , shi dai kawai abinda yake alaƙar sa da mabiyan sa wato wannan fikirar wacce sananniya ce , duk wanda ya bi shi da basirah to yasan mece ce ita kuma yasan asullanta da dokokinta da abinda yake shigar da mutum cikinta da wanda yake fitar da shi cikin ta , kuma a ciki babu mas'alar taƙlidi ballantana mazhaba ko wani ra'ayi na musamman na mutum ko rayuwar sa ta musamman , alal misali Malam (H) yana cewa : Duk wanda yace Addini (Ko Gwamnatin Musulunci ) bazai tabbata ba to fa yayi ritaya sunan sa tsohon buraza .


2  . Ni a ganina tunda har Malam Zakzakiy (H) ya fito ya bayyana shi baya kira zuwa ga wata mazhaba ta musamman kowa da kowa zai iya zuwa ya tafi dashi a kan wani sanannen hadafi , to tun anan ya kore batun lazimtawa mabiyansa bin sa a cikin duk abinda ba waccan fikirar ta Harka ba , ma'ana abinda yake yi bashi da alaƙa da mazhabar mabiyi ko mas'alolin da suke cikin mazhabar mabiyi komai da komai .


3 . A iya abinda na fahimta daga yau da gobe yanzu Harka iri biyu ce ; Akwai Harkar da Malam Zakzakiy (H) ya assasata kuma yake so ya tafi kanta har mutuwa sannan kuma yake kira a kanta kuma bayaso mabiya su sauka daga kanta , akwai kuma harkar da wasu daga cikin masu kiran kan su mabiya suma suka ƙirƙira kuma suke kira akanta saɓanin Harkar asali da yanda mai harkar asali yake a zancen sa da aikin sa , sun ƙirƙiro wasu tunanuka da Aƙidu na daban kuma sam basu da alaƙa da asalin fikirar shi Malam ɗin amma suna nunawa Duniya wannan itace Harkar kuma suna danƙarawa wasu na ciki wannan tunaninnikan da Aƙidun , in mutum ma yaja dasu a cikin abinda suke yi sai su nemi su ɓatashi ta kowacce hanya ko su nuna ma ya zama tamkar wani kafiri ko maƙiyi , kuma wannan ba baƙon abu bane a tarihin Addinai da ƙungiyoyi , har kullum akwai asalin Addini da ƙungiya akwai kuma wanda wasu daga mabiya suka ƙirkira suka danƙarawa mutane saboda jahilcin su ko son zuciyar su ko wata maslaha ta ƙashin kan su .


Misali , akwai Musuluncin da Annabi (saww) yazo da shi akwai kuma wanda wasu suka ƙirƙira suka danƙarawa mutane har yau ake yin sa in kayi ƙoƙarin musu ko saɓawa sai a kafirtaka ko a baka wani suna na daban , haka a zamanin duk Ai'immatu Ahlil Baiti (a.s) an sha samun wasu suna ƙirƙirar wani abu daban da bashi ne abinda Imamai (a.s) suke kai ba daga nan ma sai su buɗe ƙungiyoyinsu su kira mutane gare su , wanda wannan yana da akaƙa da samuwar wasu firaƙu da ake ce musu suma Shi'a ne , a kullum akwai abinda mai asalin tafiya yake yi akwai kuma yanda wasu suke ƙirƙiro tasu tafiyar da gumin su saboda wata manufa tasu ta musamman , to a Harka ma akwai irin wannan , sai ma bayan Malam (Allah ya ƙara masa tsawon rai) ya koma ga Allah za a sami wasu da za su ƙirƙiro tunanuka , Aƙidu , da ƙungiyoyi iri-iri don su ci da guminsa , Haka sunnar take duk wanda yasan tarihi da labaran al'umomi baya buƙatar ayi masa sharhin hakan .


4 . Saɓawa Malam (H) a cikin mas'alar taƙlidi ko Fiƙhu ko Tarihi ko Hadisi ko Aƙida baya nufin mutum maƙiyin Malam ne ko shi ba ɗan Harkar sa bane ko shi wani abu ne daban domin ba wannan bane ya haɗa Malam da mabiyan sa ballantana ya raba su , tunda har an bawa Kirista dama yazo a tafi dashi to maganar karba saɓawa Malam a babin Aƙida ko wata fahimta ta kau domin shi Kirista ma bai yarda da Annabcin Annabi (saww) kuma yana cewa Annabi Isa (a.s) ɗan Allah ne .


Ayatullahi Sayyid Khamene'i (H) yana saɓawa da Marigayi Ayatullahi Sayyid Khumaini (R) a cikin mas'aloli mabanbanta na Addini tare da cewa mabiyinsa ne kuma magajin sa , amma hakan bai maida shi maƙiyi ko wanda ya fita daga layin da Imam Khumainin (R) yake kai ba , bari ma har a cikin hukunci na siyasa ko gudanar da al'amura zai iya saɓawa Imam Khumaini (R) saboda shima Mujtahidi ne kuma zamanin su ya banbanta tare da duban maslahohi , to haka ilmi yake ba wai faɗa da ƙiyayya bane , shi dama ilmi a dabi'arsa ya gaji saɓani ballantana wani yanki na ilmin , kai zai wuya ka sami wani Malamin Shi'a da bai saɓawa Malaminsa ba a cikin mas'alolin Addini da rayuwa .


To haka Malamai na Allah suka rayu da almajiransu tsawon tarihi , duk yanda Ayatullahi Sayyid Baƙir Sadr ya dinga gaddamar ilmi da malamin sa Ayatullahi Sayyid Khu'i (R) bai sauya masa suna daga kasancewarsa almajirinsa ba .


5 . Duk mai bin Malam (H) dan Allah da kuma zuciya ɗaya da daidaitaccen tunani musamman wanda suke intisabi ga Shi'anci ya kamata ya fahimci wasu al'amura da a bayyane suke bamai jahiltar su ko musa su sai rafkananne ko mai son zuciya daga cikin su :


A . A cikin sharuɗɗan Harka da asalin fikirarta babu inda aka ce ga wani tsayayyen Mujtahidi da za kayi taƙlidili da shi , kana da iko kayi taƙlidi da duk wani Maraja'in Shi'a gwagwardon sharuɗɗan talƙlidi , kuma kana da ikon yin kowanne irin bincike na ilmi matukar kai ahlin binciken ne ko kayi riƙo da fahimtar wani Malami a kowacce mas'ala ta Addini matuƙar bata saɓawa asalin fikirar Harkar ba .


B . Alaƙar Malam (H) da mabiyansa alaƙa ce ta fikira da wata manufa ta musamman ba alaƙa bace ta ilmin Hadisi ko Tarihi ko Fiƙhu ko likitanci ko wata sana'ar rayuwa ta yau da gobe , mabiyi matuƙar yana da ikon yayi karatu ko yayi bincike a cikin duk wani abu da yake fanninsa ne to yana da damar hakan babu wanda ya hana shi sai ƴan bani na iya ko jahilai da masu son zuciya .


C . Malam baya buƙatar sai mutum yayi ƙarya ko camfi da khurafat wajen nuna masa soyayya , bashi kariya , bayyana matsayin sa , kasancewar sa Malami kuma bawan Allah na gari da Allah ya fahimtar da dubun dubatan al'uma tafarkin Ahlul Baiti (a.s) ta dalilin sa ya wadatar dashi daga dukkan wani matsayi da mutum zai wuce gona da iri wajen ƙirƙirar masa , shi kanshi da wannan yake alfahari  ko ina yaje a Duniya kuma da wannan Duniya ke ƙinsa ko suke sonsa , Annabi (saww) ya cewa Imam Ali (a.s) : Allah ya shiryar da mutum ɗaya ta dalilinka yafi alkhairi gareka daga dukkan abinda rana ta haska .


D . Wajibi ne ƴan Harka na gaskiya su kasa mutane kashi uku ba kashi biyu ba kamar yanda waɗanda suka ƙirƙiri harka a cikin Harka suke kasa mutane , ma'ana dole su raba mutane kashi uku :


i . Kashi na farko sune ƴan Harka ƴan uwan su waɗanda suka yarda da fikirarta kuma suke binta , ma'ana su ɗaukesu ƴan gida kuma masoya da suke tafiya tare dasu a cikin Harkar Addini da fikira duk da baki da haƙori ma ana saɓawa .


ii . Wanda ba ƴan Harka ba amma su basa faɗa da Harkar ko jagoranta , bari ma wasun su suna girmama shi suna ganin sa bawan Allah mutumin kirki , wasun su kuma sun sanshi amma basu fahimci dai mene ne hadafin sa ba kuma me yake kira akan sa , wasun su kuma sun fahimce shi amma dai basa bin sa suna dai da ra'ayi da ya saɓa nasa ba kuma wai don suna ƙinsa ko faɗa da shi bane , wasu daga cikinsu ma basa son Malam kuma basa ƙinsa bama su sanshi ba , kuma wannan sunnah ce ta rayuwa kafin Addini da ilmi .


iii . Akwai kuma waɗanda ba ƴan Harka bane kuma basa cikin kashi na biyu , bari su maƙiyan Harkar ne da jagoranta , duk da suma wasu suna yi bisa jahilci wasu kuma suna yi bisa sani , wanda a ko ina za a iya samun su ba wai sai lallai a cikin ƴan Shi'a ba , kamar yanda kashi na biyun can suma ba lallai sai a yan Shi'a ba har a ƴan Ƙungiya ko ƴan Ɗarika akwai su .


To wajibi ne ƴan harka suyi mu'amala da mutane akan wannan asasin da yanda kowa yake , ba wai su raba mutane kashi biyu ba kamar yanda waɗanda suka ƙirƙiri harka ta biyu suke yi ; Kawai ko kana tare damu ko kai maƙiyinmu ne , wanda wannan ta'addancin tunani ne irin na Wahhabiyyawa da ƴan Boko haram , in mutum bai ankare ba zai kaishi ga ta'addancin aiki da farwa mutane .


E . Wajibi ne duk wani mabiyin Malam ya farga yasan akan me yake bin Malam da kuma sanin menene ainihin alaƙarsa da Malam ba wai ya zauna wasu su dinga wasa da tunanin sa ba da sunan Harka ko kare alfarmar Malam bayan suma buƙatar su suke biya kawai ko jahilcin su suke yi da wauta da sunan Harka da Addini , dole mutum ya buɗe idon sa ko kuma ya zama taya a hannun wasu suna gara shi yanda suke so .

Wannan gaskiya ce mai ɗaci da wasu suka kasa fahimta da ganeta !!!


إنّها شقشقة هدرت ثم قرّت


✍️ Khadimu A'atabi Ali MuhammadAl-Abdul Faneey Al-kanaweey 


Shahru Ramadan 1445H / 2024 Miladiyya.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post