WAFATIN SAYYIDA RUƘAYYA ƳAR IMAM HUSSAINI (A.S)
A ranar biyar ga watan Safar Shekara ta 61 bayan Hijira, Sayyida Ruƙayya ƴar Imam Hussain (a.s.) tayi wafati .
Ance : An haifeta a shekara ta 57 bayan Hijira, (Shekaru uku kafin waki'ar Karbala) a garin Madina mai mai Alfarma.
Sayyida Ruƙayya (a.s) ta kasance tare da mahaifinta Imam Hussaini a waki'ar Karbala tana 'yar shekara uku, don haka babu shakka ta ga babban bala'i da musiba, a lokacin da aka kashe mahaifinta Imam Husaini iyalansa da sahabbansa . Bayan nan an kama ta tare da zuriyar Annabi da aka kama a matsayin fursunonin yaƙi zuwa Kufa, daga Kufa kuma zuwa Sham .
A lokacin da aka kai iyalan Annabi ƙasar Sham (Siriya) , wurin Yazidu ɗan Mu'awiyah (L) , ya yi umarni da a ajiye fursunonin a wani tsohon kango daga cikin kangwayen garin Sham, wanda ke kusa da fadarsa .
Wata rana da dadddare sai aka Sayyida Ruƙayya tayi firgit ta tashi daga barcin da take yi, tana cewa : Ina Babana Al-Hussain yake ???.... Na gan shi yanzu a cikin yanayi mara daɗi , da mata suka ji haka , sai suka yi ta kuka dama dukkan yaran da suke taare da su a wannan kango , ba a ɗauki wani lokaci ba , sautin kukansu ya game ko ina da ina .
Daga nan ne Yazidu (L ) ya tashi daga barcin da yake yi, saboda kukan da suke yi , yajishi kamar a mafarki , sai yace: Menene yake faruwa haka ?
Sai suka faɗa masa abin da ya faru, sai ya umarce su da su je wurin Sayyida Ruƙayya da kan mahaifinta da aka yanke (watau kan Imam Hussain) , dan ta ganshi . Sai suka kawo mata kan mahaifinta Imam Hussaini a lulluɓe da ƙyalle, sai aka ajiye mata shi a gabanta, ko da aka buɗe kan sai taga ashe kan mahaifinta ne a rufe , take ta ruɗe da kuka ! Tana maj cewa ;
“Ya mahaifina waye ya yanke maka jijiyoyin wuyanka? Waye ya maraitar damu ? Ya baba, wa ya rage mana a duniya bayan babu kai???
Nan take ta ɗora bakinta akan bakinsa mai albarka tana ta kuka sosai har ta dai suma, saboda tsananin kuka , ko da suka motsata sai suka tarar da ta riga ta rasu , rai yayi halinsa , Take suma suka ruɗe da kuka da alhinin wannan bala'in ,bayan bala'in da suke ciki , na waki'ar Karbala da ƙasidu Sham da aka yi . Allahu Akbar!
Bayan Sayyida Ruƙayya ta rasu an binneta a birnin Dimashƙa , kusa da masallacin Umayyawa, kuma har yanzu kabarinta na nan sananne ne ana ziyararta a inda tayi wafati .
TAMBIHI:
Kasancewar Imam Hussaini (a.s.) yana da ƴa mace mai suna Ruƙayya da ta rasu a Irin wannan rana , kuma itace take da sanannen ƙabarin da ake ziyarta, mas'alace da malaman tarihi da bincike da faifayewa suka yi saɓani akanta , tsakanin masu korewa da tabbatarwa , kuma anyi rubuce-rubuce akanta .
السلام على الحسين ، وعلى علي بن الحسين ، وعلى أولاد الحسين وعلى أصحاب الحسين ، ورحمة الله وبركاته ومغفرته.
✍️ Khadimul Ashrãf Al-Abdul Faneey Al-kanaweey
Juma'a, 5/Safar , dai-dai da 2 /9/2022 miladiyya.