Tafiyar El-Zakzaky tana burgeni, saboda shi kowa nasane, Musulmi da Kirista - Ƴar Jarida
"Ita kanta amfani da kalmar kishin Arewan kuskure ne, Yiwa kishi iyaka da muhalli ko mutane yana daga cikin abubuwan da sukaiwa tarishin ɗan Adam ta'adi. Yin kishin Arewa, Kudu ko ƙasa duk shirme ne, Falsaface ta turawa wajen amfani da ita a matsayin makamin nesa da juna, Irin wannan kishin ƙasancin ne ya raba Sudan Uku, Ya Gididdiba 'Republic of Congo', Ya haɗa Algeria da Egypt faɗa, Ya datse Nigeria biyu, Duk wani 'Civil War' a Duniya shine dalili, Kenan kishin Arewa ko ƙasanci bashi da wani amfani".
"Ba a kishin Muhalli ko ɓangare, Idan kace kana kishin Arewa Kenan Idan abu ya samu ɗan Kudu babu ruwanka? Ka fahimci yanda tasirin wannan tunanin zai zagwanye maka ganin wanda yake cikin bala'i ba damuwarka bane tunda ba ɗan yankika bane, Wannan abun yana daga manyan abubuwan da suka jefa duniya cikin masifa. Kalmomi Irinsu, Nationalism, Tribe, Liberalism, Colonialism, Imperialism, Negros, kai wani lokacin har Irinsu Humanity, Aikin turawa ne balle wasu kungiyoyin Duniya".
"Inda tafiyar Al-zakzaky ke burgeni shi kowa nasa ne Musulmi ɗan Arewa da ɗan Kudu, Kai harma da kirista jiya cikin bincike-bincikena na Gano Wani pastor Almajirinsa, Kuma mabiyi da ma'anar mabiyi ance haddashi ma aka dunga fafutukar sakinsa a shekarun Baya. Malam Cirista ma yabi wane Kai da wani tsaurin ra'ayinka na kin gaskiya kace bazaka bi ba....?"
@Ma'asumah Nigerian News update