SHEIKH ABDULHAMID BELLO ZARIYA, SHINE YA GABATAR DA JAWABI WAJAN RUFE TATTAKIN YANKIN PAMBEGUWA

 *SHEIKH ABDULHAMID BELLO ZARIYA, SHINE YA GABATAR DA JAWABI WAJAN RUFE TATTAKIN YANKIN PAMBEGUWA*




A yau Alhamis 22/08/2024 ƴan uwa almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) na yankin pambeguwa suka rufe tattakin yaumul Arba'in ɗin Imam Hussain (AS). 


A safiyar jiya laraba 21/08/2024, da misalin karfe 07:00 na safe, aka fara gudanar da wannan Tattaki, wakilin ƴan uwa na garin Bauchi Sheik Ahmad Yusuf yashi, shine wanda ya jagoran ci tafiyar, daga garin pambeguwa, inda aka isa zuwa garin zuntu, a nan aka yada zangon farkon, domin karin kumallon safe, inda tattakin ya cigaba da tafiya harzuwa maraban kubau, a nan aka sake yada zango a karo na biyu domin gudanar da sallolin azahar da kuma la'asar tare da cin abincin rana, bayan kammala salloli, matafiya sunci gaba da takawa a ƙafa har zuwa Dutsenwai, inda a nan ne aka kwana.


Wayewar garin yau Alhamis 22/08/2024 da misalin karfe 07:00 na safe Tattakin ya cigaba da ta fiya, har zuwa Garin Rahama da ke ƙaramar hukumar Soba ta Jihar Kaduna, inda a nan ne aka rufe tafiyar a wanann shekara 2014-1446


Tattakin Arbaeen ɗin Imam Hussain (AS) alamace ta tunawa da musibar da ta sami iyalan gidan Manzon Allah (W) na kashe jikansa Imam Hussain (AS), da dukkan wa ɗanda suke tare dashi a filin Karba. Tafiyar ta sami halarta dubban dubatan mabiya Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) wanda suka haɗa maza da mata, yara da manya daga sassa daban-daban wanda ya haɗa da Jos, Saminaka, Bauchi, Yola, Doguwar, Pambeguwa, Dutsenwai, Soba da sauran garuruwa.


Alhamdulillah cikin taimakon Allah (S) tun farkon fara tattakin, anfara shi lafiya kuma an kammala lafiya cikin tsari da nizami

Ma'asumah Nigerian News update

22/08/2024

#TattakinArabain

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post