SHAHADAR IMAM HASSAN AL-MUJTABA (A.S.)

 SHAHADAR IMAM HASSAN AL-MUJTABA (A.S.) 



A ranar bakwai ga watan Safar , shekara ta 50 bayan Hijira , babban jikan Manzon Allah (saww) , limami na biyu daga jerin Limaman shiriya, Karimu Ahlil baiti , Imam Hassan ɗan Imam Ali da Sayyida Fatima (a.s) yayi shahada a garin Madina .


Tun bayan yarjejeniyar da akayi tsakanin Imam Hassan (a.s) da Mu'awiyah ɗan Abi Sufyan (L), Mu'awiya ya cigaba da warware waɗannan sharuddan da aka gindaya masa , har ta kai ga yazo ya amshi caffa ga ɗansa Yazidu , a matsayin yarima mai jiran gado , wanda hakan ya saɓawa yarjejeniyar da akayi dashi. Daga cikin Sharuɗɗan shine zai ci gaba da gudanar da harkar Gwamanti , idan ya mutu to al'amari zai dawo wajen masu shi ko Imam Hassan ko Imam Hussain (a.s.) , amma bai iya cika wannan alƙawari ba . Abul Faraj ya rawaito cewa : 

Tun sanda aka gama sulhu tsakanin Imam Hassan (a.s) da Mu'awiyah (L), sai Mu'awiyah ya tara wasu mutanensa yace musu ; Sulhun da muka yi da Hassan na takeshi a ƙarƙashin ƙafata , kuma Ni ai ba don Sallah ko Azumi Ko Zakka da Hajji nake wannan rigimar ba , mulkin nan na kakannina nakeso , kuma gashi ya dawo hannuna .


Ta ɓangaren Imam Hassan (a.s ) ya shagaltu da ibada da shiryar da mutane da karantar dasu Addini na haƙika , sai ya zama Gwamanti tana hannun Mu'awiya , mutanen Allah da zuciyoyinsu suna tare da Imam Hassan (a.s) , hakan ya cigaba da ƙuntatawa Mu'awiyah (L) sosai , daga nan ya shiga kokarin ganin ya kawar da Imam Hassan (a s.) baki ɗaya don mulki ya cigaba a zuriyarsa yadda ya tsara ba tare da cikas gareshi ba .


Yayi ta sawa ana bawa Imam Hassan (a.s) guba yana sha , amma Allah yana tseratar da Imam Hassan (a.s.) daga sharrinsa , sai a ƙarshe da ajalin Imam Hassan (a.s) yayi , Mu'awiya ya biya matar Imam Hassan (a.s) don ta shayar dashi guba ƴar Rum, tare da yi mata alƙawuran da bai cika mata ba , kamar aura mata Yazidu da samun ɗinbin dukiya mai yawa . Haka ko tayi masa abinda yake so , ta shayar da Imam Hassan (a.s) wannan guba da Mu'awiya (L) ya bata , lokacin da Imam Hassan (a.s) yake ƙoƙarin bude baki yayin da yayi Azumi . 


Daga nan ne wannan gubar ƴar Rum ta kwantar da Imam Hassan (a.s) na ƴan wasu kwanaki , tana yawo cikin jininsa da jijiyarsa da namansa , har ta kai ga ta fara farfasa masa ƴaƴan hanjinsa ! Imam Hassan (a.s) ya dinga aman jininsa da hantarsa saboda ƙarfin wannan gubar da tasirinta, daga ƙarshe yayi wasiyyoyi ga ɗan uwansa Imam Hussain (a.s) , sannan ya koma ga Ubangijinsa a matsayin shahidi abun zalunta .Allahu Akbar !!!


An rawaito cewa ; Lokacin da Imam Hussain (a s.) ya ɗauki gawar Imam Hassan mai tsarki, da nufin binneta a maƙabartar Baki'u kamar yanda Imam Hassan (a.s) yayi masa wasiyya , cewa ya fara kaishi wurin Annabi kakansa suyi bankwana , sannan ya tafi dashi can ya binne shi a kusa da kakarsa Sayyida Fatima Bintu Asad. Sai Marwan Binil Hakam (L) ya ɗebo yaransa Umayyawa suka tare Imam Hussain (a.s) a hanya , suna tsammanin zai binneshi kusa da Annabi (saww) ne , suna cewa ai muma ba'a bari mun binne Usman bn Affan a kusa da Annabi ba don haka kuma baku isa ba .

Da labari ya isa ga matar Manzon Allah (saww) , Aisha bintu Abi Bakr, sai ta hayo kan Alfadara kamar yanda ta hau raƙumi a yaƙin Jamal , tazo tana cewa ; Nima bazan yardaa ku binne min wanda banaso ba a ɗaƙina ba sam , wuri ya yamuste da rikici da hayaniya , har ta kai ga an fara harbin gawar Imam Hassan (a.s) da kibiya ! Sai Imam Hussain (a.s) ya aiwatar da wasiyyar ɗan uwansa Imam Hassan (a.s) , ta kar ya bari a sheƙar da jini a lokacin jana'izarsa , take suka juya aka tafi can Maƙabartar Baƙiy , aka binne Imam Hassan kusa da kakarsa Sayyida Fadima Bintu Asad (Mahaifiyar Imam Ali ) tsira da Amincin Allah su ƙara dawwama a gare su baki ɗaya .


Kafin Imam Hasan (a.s) ya cika , a ko da yaushe Imam Husain (a.s.) yana shiga wajensa , har suyi ta kuka da jimamin halin da suka shiga tun bayan rashin kakansu Annabi da Mahaifansu , Imam Hasan (a.s) ya kasance yana cewa ; Wannan ne abinda kakanmu Manzon Allah (a.s) yace zai samemu , lallai ya gaskata a cikin zancensa .


Imam Hassan (a.s) ya rayu tsawon shekaru 47 , tare da Imamancin Shekaru goma , tun bayan Shahadar mahaifinsa Imam Ali (a.s.) a shakara ta Arba'in (40) bayan hijira , shi kuma Imam Hassan ya rasu a ranar bakwai ga watan Safar shekara ta Hamsin bayan Hijira , A wata ruwayar kuma ; 28 ga watan Safar ne ranar shahadar Imam Hassan (a.s.) .


السلام عليك أيها المظلوم الشهيد ورحمة الله وبركاته ومغفرته


✍️Khadimu A'atabi Ali Muhammad Al-Abdul Faneey Al-kanaweey 

7 / Safar/ 1444H - 24/8/2023 Miladiyya

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post