MU FA MASU GULUWI DA ƁATAR DA MUTANEN NAN MUNA GANIN SU A IRAƘI IDO DA IDO DA YANDA SUKE YI !!!
Kana zaune a ƙofar gida ko idan ka shiga motar haya (Taxi) ko kana cikin tafiya sai kawai a miƙo maka zungureriyar takarda ace gashi nan ka karanta , a ɗan fara yaudararka da hira da kuma sunan Imam Mahdi (a.j) kaza da kaza, can sai kaji ance mu mabiyan wane ne (Misali Ahmad bin Hasan bin Gâdeh ) wakilin Imam Mahdi ko ɗan Imam Mahdi ko imanin wannan zamanin a zahiri don haka ana maka albushara da kazo kayi mubaya'a , ko a yaudareka da ƙudi ko falalolin ƙarya , bayan shi shugaban nasu ma baya Iraqin yana can Dubai a zaune neman sa ake ruwa a jallo , idan suka fahimci ɗalibin ilmi ne kai za ka musu jayayya sai su hau zaginka da tsinewa Maraji'ai wai ku kuka hana a fahimci Imam Mahdi a bi shi , ko su ce maka ka dena Taƙlidi haramun ne kazo kabi tafiyar su ita za ta sadaka da Imam kai tsaye .
Idan ka duba takardun da suke rabawa za kaga riwayoyin Ahlil Baiti (a.s) da Ayoyi ne aka musu muguwar fassara aka juya sama ta koma ƙasa tare da yi musu tafsiri irin na ƴan haƙiƙa riwayar tayi gabas su sunyi yamma kai kace Anisi ɗan Faira , sukan samu mai motar haya su biya shi ko a kyauta ma suce duk wanda ya hau ka ba shi ko mai su bawa mai kanti ko a samu wasu wawayen matasa su dunga yawo a babur suna raba takardun Guluwin nan , kamar yanda suna da shafuka dayawa a kafafen sadarwa da suke yaɗa da'awar su ko a maka text ta "Messenger" ace kazo kabi wane shine Imam Mahdi a yau idan kayi jayayya su fara cin mutuncin ka ko su kafirta ka , suna nan ƙungiyoyi daban-daban muna ganin su , kuma duk ɗalibin da yake zaune a Iraqi zai wuya bai san hakan ba .
Hatta a cikin mabiyan Sayyid Muƙtada Assadr akwai masu aƙidar cewa shine Imam Mahdi ko shi Annabi ne da aƙidu na guluwi da jahilci da wauta iri-iri duk da dai yakan musu magana wani lokacin amma makauniyar soyayya da biyewa aɗifa zallah da son rai sun rufe musu ido , kamar dai Gulatun zamanin Imamai (a.s) , wanda zafin kan nan na su yake kai su ga ta'addanci , sai kawai kaga sunje gidan mutum sun masa aika-aika da makami don kawai ya saɓa musu ko ya musu nasiha .
Don haka ne muke ankarar da ƴan uwa muminai da suyi hattara da wanda zai zo ya ribace su da sunan yaɗa fikra ko taimakon Harka da Jagora (H) , amma ba wai muna so muyi suka bane ko makamncin haka , a'a , nusarwa ce akan illar hakan da ka iya maida mutum ɗan ta'adda a aiki da tunani , gyara kayan ka dai baya zama sauke mu raba .
✍️Khadimul Ashrãf Al-Abdul Faneey Al-kanaweey