Me kashe Sarkin Gobir ke nufi ga tsaron Najeriya?
A ranar Laraba al'umma sun kaɗu game da labarin kisan da ƴan bindiga suka yi wa Sarkin Gobir na Gatawa Isa Bawa, bayan kwashe makonni a hannun ƴan bindiga.
Lamarin na zuwa ne kimanin mako ɗaya bayan sakin wani bidiyo da ya riƙa yawo a shafukan sada zumunta, wanda ya nuna sarkin a hannun masu garkuwa da shi yana roƙon gwamnati da iyalansa su cece shi daga hannun ƴan bindiga.
Duk da cewa ƴan bindigar sun kwashe shekaru suna kashe-kashe a yankin na arewacin Najeriya, amma ba kasafai ake samun irin haka ba.
Sai dai sau da yawa bayan an gama jimami, lamarin sai ya kwanta sai kuma idan wani lamarin makamancin haka ya sake faruwa a gaba.
Gwamnatin Najeriya dai ta daɗe tana cewa tana bakin ƙoƙarinta wajen shawo kan matsalar ta ƴan fashin daji, to amma abin na ci gaba da addabar al'ummar jihohi da dama.
Su ma gwamnonin jihohin na iyakar bakin ƙoƙarinsu ta wani fannin.
Tuni gwamnatocin jihohin yankin irin su Katsina da Zamfara da ita kanta Sokoto suka ƙaddamar da rundunonin ƴan sa-kai na jihohi domin shawo kan matsalar, amma har yanzu babu jihar da aka kawar da matsalar baki ɗaya.
'Sarakuna na cikin hatsari'
A tattaunawarsa da BBC, shugaban kamfanin Beacon Consulting, mai nazari kan tsaro a yankin Sahel, Kabiru Adamu, ya ce wannan lamari ya ƙara fito da hatsarin da sarakunan yankin arewa ke ciki.
Ya ce, “Akwai daga cikin ɓangaren gwamnati waɗanda suke da fahimtar cewa daga cikin abubuwa da ƴan bindigar nan suke so har da kawar da sarakuna, dalilin da suke cewa haka kuwa shi ne cikin burinsu har da kafa tasu daular, kuma babu yadda za su tafa tasu daular ba tare da sun kawar da sarakunan ba."
Sai dai wani abu shi ne a baya, hukumomi sun sha sanar da cewa an gwano wasu masu sarautun gargajiya da hannu a matsalar tsaro ta ƴan fashin daji.
To amma Kabiru Adamu ya ce sarakunan na daga cikin mutane da suka fi fuskantar barazana a wannan yanayi na rashin tsaro.
“Babu shakka suna cikin hatsarin kuma muhimman abu ne su fahimci cewa suna cikin hatsarin su ƙara inganta irin tsaron da suke tare da su."
Wasu buƙatu baya ga kuɗi
Bayan yin garkuwa da sarkin Gobir na Gatawa, abin da mutane suka sani shi ne ƴan fashin dajin sun buƙaci a biya su kuɗi kafin a karɓo shi.
Kuma abin da mutane suka yi tunani shi ne ana ci gaba da ƙoƙari ne na tattara kuɗin da za a karɓo sarkin.
To sai dai Kabiru Adamu ya ce wannan ba ita ce babbar buƙatar da ƴan bindigar suka gabatar ba.
“Akwai bayanai da ke nuna cewa waɗanda suka kama shi ɗin sun so a yi musayar fursunoni, wato akwai ƴan'uwansu waɗanda bayani ke nuna cewa sun dawo daga aikin Hajji aka kama su, to cikin buƙatun da suka gabatar, sun ce dole ne a sakar musu ƴan uwansu," in ji Kabiru Adamu.
Bayanin Dakta Adamu ya nuna cewa rashin biya wa ƴan fashin buƙatunsu na yin musayar fursunoni ne ya sanya suka fusata suka kashe sarkin.
Ko a lokutan baya an sha zargin faruwar irin hakan, sai dai ba kasafai lamarin kan fito fili ba, musamman idan idan aka sace mutane masu yawa ko kuma ɗalibai.
@ma'asumah Nigerian News update