MALAMA ZEENATUDDEEN IBRAHEEM A SHEKARU 63
Ranar Juma’a 14 ga watan August, Malamarmu, kuma uwarmu, uwargida ga Jagoranmu, Malama Zeenatuddeen Ibrahim ke cika shekara 63 daidai da haihuwarta.
An haifi Malama Zeenah ne a ranar 14 ga Agusta a shekarar 1961 a unguwar sabon gari da ke Zaria. Inda ta yi karatunta na firamare zuwa sakandire a tsakanin Zaria da Katsina, sannan kuma ta dawo Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria ta karanta fannin aikin banki.
Saboda harkar gwagwarmaya, Malama Zeenah bata samu dammar kamala wannan karatun ba aka kore ta. Sakamakon wani rikici da aka yi da su akan kawo giya dakin taro na Congo Conference hotel, su kuma su Malama a lokacin sun sha alwashin in har aka kawo giya wajen sai sun lalata ta. A yayin da hukumar makarantar ta musu barazanar koransu daga makarantar idan har sukai hakan. Lalalai kuwa abin da ya wakana kenan. Sai ya zamana sun kafe akan ba za’a kawo giyan ba, kuma da aka kawo suka bata ta, aka tambaye su suka amsa su suka yi, sai hukumar makarantar ta kore su daga makarantar kwata-kwala.
Bayan wannan waki’ar ne, sai Malama Zeenah ta tafi karatun Hauza a Jamhuriyar Musulunci ta Iran a tsakanin shekarar 1982/1984. Wanda kamar yadda ta ke fada, ko da suka je Hauza din sai suka tarar duk abin da ake koya musu a wajen Malam (H) ya riga ya koya musu shi a wajen Ta’alimat da yake musu a wancan lokacin.
Malama Zeenah ta fara jin wa’azin Jagora (H) ne a shekarar 1977, kimanin shekara 38 kenan yau, a wajen wani IVC da aka yi a wannan shekarar a garin Potiskum. Sai dai kamar yadda ta ambata, a wannan lokacin Malam bai santa ba. Sai a shekarar 1979 a lokacin ne ta samu labarin za’a yi wani taro a garin Lagos, inda kuma ta samu halarta, sannan daga nan ma aka dawo Bauchi akai wani taron. To a nan ne farkon lokacin da Malam ya ganta.
Malama ta kasance ita kadaice mace da ta fara halartan Muzaharar farko a wannan Harka, wannan Muzaharar da aka kira “Islam Only”, wato Musulunci Kawai, wanda aka yi a shekarar 1980, wanda take kunshe da bayyana bara’a ga tsarin kafirci da yi wa kira izuwa ga komawa bin tsarin Allah wilaya.
Har wala yau, Malama ta fuskanci jarabawa mai tsanani daga wajen iyaye, musamman mahaifinta saboda wannan harkar, saboda shi mahaifin nata a lokacin Dan Dariqa ne, to kuma in za ku iya tunawa a wannan lokacin ne Izala ma ta bullo, sai ya zama wasu na zuga shi akan wannan Harka din ma da yarsa ke yi Izala ne, alhali kuma shi baya son izala. Sai ya zama hatta Hijabi da take sakawa, mahaifin nata yakance bai taba ganin wata mace da Hijabi ba. Abin day a sani kawai matar aure ne kan saka gyale, amma budurwa da wannan lillibi kamar mai ciwo a wuya. Da sauransu.
Wanda ta nan za mi iya fahimtar cewa duk wani wanda ya ga Hijabi, ko Uwarsa taga Hijabi ta fara sakawa a tsawon shekaru 40 baya, to sun samo ne daga wannan Harkar, a yayin da Malama Zeenah ce asasinsa!
Saboda gudun tsawaitawa, ba zan kawo maganar auren Malama da Jagora (H) ba. Duk da cewa zaka sha mamakin yadda wannan maganar aure ta faru da abubuwan da suka biyo bayan hakan har zuwa lokacin amincewar Malama akan auren zuwa yinsa. Kamar yadda Malama ke fada, tun a shekarar 1981 Malam ya mata batun yana son aurenta, da rashin amincewarta zuwa amincewarta bayan mafarkai biyu da tayi mai cike da ishara akan hakan, wanda har Allah ya kai ga yin auren a shekarar 1984.
Wata biyar da yin aurensu Janar Muhammadu Buhari ya kama Malam Zakzaky (H). ki gwada da kanki yak e ‘yar’uwa, ace kuna ganiyar amarcinku a zo a kama miki angonki, ya zafin hakan yake? Zan so masu karatu su koma ga labarin yadda wannan kamun ya kasance don su ga darussa masu yawa a cikinsa ta yadda hatta a ranar da aka zo kama shi din shi ke girka musu towon da za su ci a ranar.
Hakika tun daga nan Malama ta fara fuskantar jarabawowi manya-manya a gidan mijinta saboda wannan Harkar. Ta yadda takaima ga tun da a wadancan shekarun ana kama mijinta, har ita a kama da yaranta, a duketa, har an taba marinta da sauransu, hart a kaima ga an wayi gari rana daya aka kashe mata ‘ya’yanta guda uku masu daraja. Hakika manya-manyan darajoji suna tare da manya-manyan bala’o’i!
Ban son tsawaita rubutun, duk da cewa na tsawaita din. Amma ina mai shawartan ‘yan’uwa da su koma ga littafin da kamfanin ALMIZAN suka buga a shekaru 7 da suka gabata, wanda suka kawo hirarrakin da suka yi da Malam (H), almajiransa, danginsa da yayansa da sauransu a ciki. Sun ma littafin suna “SHEKARU 67 MASU ALBARKA”, su karanta hirar da aka yi da Malama Zeenah tun daga shafi na 28 har zuwa shafi na 45 ya sha karatun tarihin wannan baiwar Allah din daga bakinta, ta yadda zamu dauki darussa masu yawa daga cikinsa a yayin da muke wannan Harkar ta yunkurin tabbatar da addinin Musulunci.
Ga wanda ba shi da wancan littafin, yana iya duba lillafin da Malam Muhammad Sulaiman Kaduna ya wallafa shekaru 5 dasuka wuce mai suna “Tarihin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) da Harkar Musulunci” sai ya duba ya nakalto wannan hiran tun daga shafinsa na 97 har zuwa shafi na 132. Ko kuma ya bincika jaridar Almizan din watan Sha’aban 1432 don ya sha karatun wannan hirar da ALMIZAN tayi da Malamar.
Muna taya Malama murnar cika wannan shekaru masu albarka, wadanda an yi su ne a cikin gwagwarmayar addini kuma Alhamdulillah har yau ba’a sauya ba sai ma abin da ke karuwa. Muna miki fatan Allah ya kara tsawon kwana da yardarSa gareki, ya kuma tabbatar da ked a mu baki daya har zuwa riskar ajalinmu.
Tare da dubun godiya da fatan alkairi ga masu karatuna. Wassalamu alaikum wa rahmatullah.