DA GASKE NE WATAN SAFAR WATAN BALA'I NE , BASHI DA ALKHAIRI DA ALBARKA ???

 DA GASKE NE WATAN SAFAR WATAN BALA'I NE , BASHI DA ALKHAIRI DA ALBARKA ???



Kamar yanda yake a al'adar mutane a ƙasar Hausa , dama larabawa da wasu al'ummatan Musulmi sukan camfa watan Safar , suce ; Wata ne da na saukar da bala'ai da musibu kan mutane ,bashi da albarka , wata ne nahisi, a cikinsa akwai larabgana . Wasu al'ummatan ma basa yin abubuwa na rayuwarsu da yawa a cikinsa , kamar aure ko tarewa a sabon gida , ko ziyaratar mara lafiya da sauransu .

Ya zama ba abinda suke yi a wannan watan face , shiga firgici da tashin hankali , da aikata wasu al'adu na camfi da maguzanci da basu da asali da sunan neman kariya da mafita daga sharrin wannan shu'umin wata (Na Safar , kamar yadda suke faɗa) . Abun tambaya anan shine , shin da gaske duk waɗannan abubuwan da ake faɗa ko tsammani ? A matsayin mu na Musulmi (Mabiya Ahlul Baiti) mene ne matsayar su da Addininmu game da hakan ?


AMSA : 


Tabbataciyya magana mai inganci , duk waɗannan maganganu da abubuwan da mutane suke yi a watan Safar , basu da wani asali a Addini, Camfi ne da shu'umanci da maguzanci irin na mutanen jahiliyya , kamar yanda yake a wajen kowacce al'umma , suna da abubuwa na camfi da suke camfawa , kamar larabawa tun zamanin jahiliyya sukan camfa wasu dabbobi, tsuntsaye, ranaku , lokuta kamar watan Safar misali , shi yasa har yaƙi suna farashi ne a cikinsa Safar, haka muma Hausawa muna da wannan abubuwan dayawa , wanda gado ne na maguzanci .


Dukkanin su basu da asali , sun saɓawa karantarwar Addini da Ahlul Baiti (a.s.) , riwayoyi da yawa sunzo da suke hani da camfa wasu ranaku ko lokuta ,Annabi (saww) yana cewa : Duk wanda yake camfi da sihiri da bokanci baya tare dashi . Kamar yanda babu wani dalili tabbatacce da yake nuna cewa an ware wani wata daga cikin watanni goma sha biyu (12) da ake da su a matsayin watan bala'i da bashi da albarka da alkhairi. Hasali ma shi wannan watan na Safar ana masa lakabi da Safar ɗin alkhairi (صفر الخير)ko Safar ɗin Nasara (صفر المظفر) , kamar yanda galibi malamai suke rubutawa a rubuce-rubucen su . 


RIWAYOYI DA DALILAI


Haka nan , ruwayoyin da wasu ke kawowa game da Camfa watan safar da rashin alkhairin sa basu da wani asali da inganci , riwayoyi ne ƙirƙirarru , Umayyawa da aka cusasu cikin litattafan Addini , ko ake dangantawa Annabi da Ahlinsa (a.s) , wanda haramun ne ga mutum danganta musu hakan domin bai tabbata ba . Haka duk dalilan da wasu suke ƙoƙarin jingina dasu wajen Camfa watan Safar , kamar ayoyi basu da inganci a wajen Ahlin ilmi da tahƙiƙi .


MAI LITTAFIN MAFATIHUL JINAN DA WATAN SAFAR 


Tayu wani yace ; Ai a cikin littafin Mafatihul Jinan Sheik Abbasul Ƙummi ya yi magana akan cewa , watan Safar wata ne Nahisi har ya kawo addu'ar tsari , a farkon A'amal na watan Safar , ya zamuyi da wannan?


Sai ince : Eh hakane, ba haka bane . Abinda nake nufi hakane shine , tabbas Almuhaddisul ƙummi ya kawo magana cewa , watan Safar Nahisi ne , amma abinda yace shine : Ka sani wannan wata na Safar wata ne da ya sanu da Nahisanci (Rashin alkhairi da bala'i) , sai ya kawo addu'a . Amma abinda nake nufi da ba haka bane shine ;

 Sheik Abbas ba yana tabbatar da cewa wannan camfe-camfen na mutane hakane suna da inganci ! A'a , yana faɗar abinda ya shahara ya sanu a wajen mutane ne , kuma dama ba komai bane da ya shahara yake daidai ko tabbatacce (رب مشهور لا أصل له) , shi yasa ya kawo wannan addu'ar ta (يا شديد القوى) , ya kuma ce mutum yayi sadaka da isti'azah , saboda akwai mutanen da ko da sun san cewa abu camfi ne , ransu baya nustuwa saboda sabo da al'ada da kuma yadda abun ya zame musu jiki , shi yasa ake basu addu'a suyi , amma ba wai don abun haka ne , kuma dama ita addu'ar neman tsari da sadaka ai ana yin su a kowanne wata dan neman tsari da mafita , ba wai sai a iya watan Safar ba .


Sannan kuma dama ba ana kore cewa bala'i ko wani abu mara daɗi bazai iya faruwa ba a watan Safar , sai dai cewa babu wani dalili bai kuma tabbata ba , ware wannan watan ko wata rana a cikin sa , a camfasu da bala'i ko rashin alkhairi, don haka babu wani ishkali a cikin addu'a da maganar Sheikh Abbasul Ƙummi (Rahimahullah) .


MUSIBUN AHLUL BAITI (A.S.) DA WATAN SAFAR 


Tayu wani yace ; Ai kuma a watan Safar akwai munasabobin juyayi da alhini na abinda ya sami Ahlul baiti (a.s) , shin hakan bai da alaƙa da rashin albarka da wancen camfi na mutane keyi ga watan ba ???


Shima dai zamu masa ; Eh , kuma a'a . Lallai wata ne na alhini da juyayi ga abinda ya samu Ahlul Baiti na musiba kamar Almuharram, domin a cikin sa ne ake Arba'in , Imam Hassan yayi shahada, da Imam Ridha da Manzon Allah (sawa) , dama wasu abubuwa na alhini , ana so ayi juyayi da makoki , amma kuma hakan baya nuna cewa watan bai da albarka ko alkhairi bare a camfa shi . 


In da za'a Camfa shi saboda wannan dalilin to watan Almuharram ne yafi cancanta da hakan , domin shi watan Safar akwai abubuwan farin ciki da suka faru cikinsa , kamar haihuwar Imam Musal Kazim , da auren Annabi da Nana Khadijah (a.s) da sauransu , saɓanin watan Almuharram da shi babu wani abun farin ciki da murna da ya faru a cikinsa .


RUFEWA


A takaice dai , batun cewa watan Safar bashi da albarka ko watane na saukar bala'i ga mutane , da Camfa shi , da yin wasu abubuwa na maguzanci a ciki , abuna bai da asali , bai da alaƙa da Addini , kuma baya halatta yinsu da yaɗasu da imani dasu , ya zama wajibi ga mumini ya ƙaurace musu yayi watsi dasu .


MAFITA 


Mutum ya dogara ga Allah , ya yawaita neman tsari a cikin kowanne wata ba iya Safar ba , ta hanyar yin Addu'oi Ma'asurai da sadaka da karatun Aljur'ani.


Kuma ya zama wajibi mu sani Ahlul Baiti (a.s) sun yi hani da yin imani da yarda da waɗannan abubuwan , har a wasu ruwayoyin sun kwadaitar da yin aiki da sakankancewa a Larabar ƙarshe ta wata (Safar) , duk dan su yaƙi waccen al'ada ta jahiliyya da mutane ke Camfa rana ko watan Safar, ba rana ko watan Safar ba har awanni sun hana a zage su ko a la'ance su .


Ba dan tsoron tsawaitawa ba , da mun kawo Nassi na ruwayoyi da maganganun Malamai akan wannan mas'alar, mun wadatu da iya abinda muka rairayo daga waɗannan riwayoyi da maganganun Malamai saboda takaitawa , In sha Allah.


Wasallamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu 👏


✍️ Khadimul Itrah Al-Abdul Faneey Al-kanaweey 

Asabar , 6/Safar /1443H - 3/Satumba/2022 Miladiyya.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post