Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga Dakta Muhammad Tahar Adam (Baba Impossible) Daga: Hashim Badikko, Kaduna.

 Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga Dakta Muhammad Tahar Adam (Baba Impossible)



Daga: Hashim Badikko, Kaduna.


Baba impossible fatan kana lafiya. Bana son in ɓata maka lokaci da dogon bitan karatu. Idan ban mance ba wannan ita ce wasiƙa ta biyu zuwa gare ka tun bayan makircin da ka kullawa Dakta Sheikh Abduljabbar Sheikh Nasiru Kabara.


Na sake rubuta maka wannan wasiƙar ne ganin yadda na ɗauka ce wa ko kunyar duniya za ta ishe ka, ka saduda, ka tuba, ka kuma neme yafiya, sannan ka jira hukuncin Allah, amma sai na ga ka zama Yahudu, tuba babu.


Wannan wasiƙar ta wa kai tsaye tana da alaƙa ne da wani bidiyonka da na gani yana yawo a social media wanda ake wa take "Ka daure ka kalla sannan ka yaɗa". Bayan na kalli bidiyon wanda a ciki kake kira ga Malaman Maja su sake haɗuwa domin ɗaukar mataki irin wacce ku ka ɗaukarwa Malam Abduljabbar akan ɗaya daga cikin Malamanku na maja! bayan na kalli faifan bidiyon ban ga wani abu sabo ba wanda ba na tsammanin gani ko ji ba (The devil is still the same). Bayan ka yi nasarar tura Malam Abduljabbar kurkuku da taimakon mai gidanka (Ganduje) da mataimakansa; ka ci gaba da bin Malam da sharri da kuma yarfe domin ka ci gaba da ɓoye mummunan aikin da ka yi masa na sharrin cewa yana zagin Manzon Allah (sawa). 


A sanin da na yi maka, tun daga faruwar zaluncin da ku ka yi wa Dakta Sheikh  Abduljabbar Sheikh Nasiru Kabara (Wanda ka zama Ummul Khaba'is), ba na tsammani wani alheri zai iya fitowa daga gare ka, ko kuma aji ka yi magana cikin hayyaci. Annabi (sawa) ba wasa bane.


Baba impossible! Ina da tabbacin ce wa da yardar Allah ba za ka taɓa samun kwanciyar hankali ba a duniya. Ka keta halarar da babu wanda zai yi wasa da ita face sai Allah (swt) Ya keta shi (Wato Halarar Manzon Allah sawa). Masoyin Manzon Allah (sawa) da Iyalan Gidansa  Tsarkaka na kololowa, ka juya masa zance zuwa makiyin Manzon   Allah (sawa), kuma ka ci gaba da yaɗawa.


Baba impossible! Ka jagoranci zaluntar Malam Abduljabbar. Kai ka kitsa, ka tsara, ka jagoranta, ka kuma zartar masa da hukunci. Ka ɗauka ce wa yadda ka yi nasarar ɓoyewa mutane mummunan shirinku ga Dakta Abduljabbar; za ka iya boyewa Allah. hmmm! _miskeen._ 


Mun gode wa Allah. Kun sanarwa da duniya cewa Malam Abduljabbar bai amsa tambayoyin diraman da ku ka yi masa ba, sai ga shi bidiyoyi suna ta bayyana na irin wasan kura da yi wa Malaman diramanku _(Ƴan Majawood),_ bayan kun hana shi dauƙa da na shi na'uran bidiyo kamar yadda ku ka alƙawarta masa.


Malamin da ya shahara da bayar da kariya ga Janábin Manzon Allah (sawa) da Iyalan Gidansa Tsarkaka, wanda zai yi wahala ka ƙirga mutune uku a nageriya wanda suka shahara da baiwa Manzon Allah (sawa) kariya ba ka sako shi a ciki ba.


Baba impossible! Shiga gidan kurkuku ba ƙasƙanci bane ga Malami, domin manyan bayin Allah sun shige ta, wasu ma  a ciki suka mutu. Kurkuku ga bayin Allah ɗaukaka ce.


Baba impossible! Na ɗauka wulakancin da ka fara gani daga iyayen gidanka (Ganduje) na korar kare da wulakancin da su ka yi maka daga gwamnati, da kuma su kan su satar da aka fara kama su da ita zai sa ka fara tunani ce wa lokaci yana ƙure maka ka sake tunani.


Baba impossible! Tsofa ya yi gardama. Ka kasa banbance harkar bori da kuma Musulunci. Mu fa ba mu da alaƙa da tsafi da maita. Ba mu da matsala da kai inda  tsunburbura ka ce Dakta Abduljabbar ya zaga (Saboda su ne abin da aka san ka da su). Amma ka shiga rigar Musulunci ka jinginawa Malami ƙaryar ce wa ya zagi Manzonmu, Manzon Musulunci.


Baba impossible! Ina baka tabbacin ce wa al'umma sun daɗe da gane cewa ƙarya ku ka jinginawa Malam, ga shi an fara ganin ku a rana kuna tonawa kan ku asirin ce wa ba fa muƙabala aka yi ba, har kuna  tsinewa juna a mimbarorinku tun ba a yi ma yi nisa ba.


Baba impossible! Ka yi nasarar raba iyaye da ƴaƴayensu. Ka yi nasarar raba wasu mataye da mazajensu. Ka yi nasarar raba zumunci da ƙarerayinka na cewa Shugaban As'habul Kahfi yana cin zarafin Shugaba (sawa). Amma ina son in ba ka tabbacin cewa nasarar ka (temporary) ce. Domin gaskiya za ta yi halinta. Maulana Dakta Sheikh Abduljabbar Sheikh Nasiru Kabara (Ameerul Wa'izeen), kuma (Sarkin Gida) zai yi FREE! Zai samu ƴancin sa, tare da baƙin albishirin da zai fito muku da su (Na littattafai).


Baba impossible! ka yi naka, ka saurari na Allah...

وَالْعَاقِبَةُ لِلْمُتَّقِينَ 


-HASHIM BADIKKO  Hashim Badikko 

16/08/2024.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post