AL-MARHUM SHAIKH ADAMU TSOHO AHMAD A cikin Alkur’ani Mai Girma, Allah Ta'ala yana cewa:

 AL-MARHUM SHAIKH ADAMU TSOHO AHMAD 



بسم الله الرحمن الرحيم


 يَا أَيَّتُهَا النَّفْسُ الْمُطْمَئِنَّةُ, ارْجِعِي إِلَى رَبِّكِ رَاضِيَةً مَرْضِيَّةً, فَادْخُلِي فِي عِبَادِي وَادْخُلِي جَنَّتِي. 

صدق الله العظيم.


A cikin Alkur’ani Mai Girma, Allah Ta'ala yana cewa:


وَبَشِّرِ الصَّابِرِينَ, الَّذِينَ إِذا أَصابَتْهُمْ مُصِيبَةٌ قالُوا إِنَّا لِلَّهِ وَإِنَّا إِلَيْهِ راجِعُونَ.


“Ka yi bushara ga masu hakuri, wadanda idan wata Musiba ta same su, sai su ce, daga Allah muke, kuma gare Shi muke komawa.”


Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un.


Babu shakka rashin Al-Marhum Sheikh Adamu Tsoho Ahmad babban rashi ne ga duniyar Musulmi da Musulunci bakidaya, musamman a wannan nahiyar ta Afirka.


Musulmi sun yi rashin Malami mai karantarwa, mai shiryatarwa, mai tsoron Allah tare da kamewa, mai hakuri da saukin hali, mai tausasawa tare da afuwa, mai juriya tare da dakewa, mai kyauta tare da girmamawa, ma'abocin karamci da natsuwa, mai tsantseni da wadatuwar zuci, wanda ya nasu da kyawawan dabi'un Annabi (S) da Ahlulbaiti (AS), har aka wayi gari kallonsa da mu'amala da shi ko yaushe kan tunawa mutum Allah Ta'ala ne.


Shaikh Adamu Tsoho, mutum ne da aka masa shaidar tsananin hakuri da yafiya da shanye damuwa, kila ma shi yasa a tsawon shekaru ya rika fama da jinyar ciwon zuciya, kuma a hakan, shi ke lallabawa da rarrashin bayin Allah, akan hakuri da dakewa a tafarkin Allah, da hakuri da yanayin rayuwa, da hakuri da duk inda Allah Ta'ala Ya ajiye mutum, da hakuri akan abin da Allah Ta'ala Ya azurta kowa na halal, da hakuri da juna, da hakuri da karan kai.


Malami ne, wanda tun tasowarsa, har rasuwar sa a ranar Talata 24 ga Al-Muharram 1446 (30/7/2024) bashi da abokin da ya kai littafi. Uwargidansa, Malama Husaina ta fada min cewa, ko bacci ya farka da daddare, ko in damuwa ta ishe shi ya kasa bacci, ko in yana ciwon da ba zai iya tashi ba, ya kan dauko littafi ne ya fara karatu. Ni shaida ne, tsawon shekaru muna tafiye-tafiye da shi, ba mu taba tafiya wani gari ba, face akwai littafi da yake bitansa a cikin mota. Ban taba shiga na same shi a cikin falonsa ba, face yana dayan abubuwa guda uku; ko dai sallah, ko addu'a, ko kuma karatun littafan addini.


Don haka, kamar yadda kullum yake cikin karatu, haka kuma kullum baya gajiya da karantarwa. Ban san wani wakilin 'yan uwa almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) da ke karantar da littafai daban-daban kamar Al-Marhum Shaikh Adamu Tsoho ba. Akalla a kwanakin kowane mako guda bakwai yana ba da Ta'alimi a ranaku hudu ko biyar ga yan uwa, na littafan ilimi daban-daban. Kuma ko bai da lafiya in har ba jikinsa ya ƙi bashi damar tashi ba ne, zai je ya bayar da karatun nan ko da yana numfarfashi.


Kuma kullum cikin karfafa 'yan uwa yake akan karatu, a san addini, a fahimci addini, a bautawa Allah Ta'ala a irin yadda Allah din ya tsara, wanda kuma baka iya fahimtar hakan sai ka yi karatun addini. Don haka, ni shaida ne akan karfafawansa, domin an yi lokacin da ya saya min littafai da kudinsa, wasu da ba a samunsu ma ya rika badawa ana 'Photocopy' dinsu, sannan kuma ya rika zaunar da ni yana biya min su, ta yadda akan iya shafe awa guda yana karantar da ni littafi ba tare da ya nuna gajiya ba, har sai na ce ya isa haka Abbah.😢


Ya yi iyakan kokarinsa wajen ganin an taskace karatuttukan da yake gabatarwa, don ya zama ba wadanda ke gabansa ne kawai za su amfana da shi ba, har da al'ummar duniya gabadaya, da kuma musamman wadanda za su zo a bayansa. A irin haka ne, Shaikh Adamu Tsoho ya rika ba da dama, akan dauki karatunsa a kowane hali aka bukata, har ya zama ta janibina nasan akwai karatun Bahasin Akhlaq da muke fara yinsa daga karfe 12 na dare, lokacin babu hayaniya, mu kare karfe 2 na dare a cikin falonsa.


Baya taba nuna ƙosawa da mutane, in ka ziyararce shi da nufin gaisuwa, ko tambaya, ko neman sani, ko rokon wani abu ma, ba zai taba nuna maka ya gaji da zama da kai ba, zai zauna a inda kuke ko za ku shafe awanni, har sai in kai ne ka lura da yanayinsa, kace insha Allah Malam, in ka nuna alamun bukatar a rabu, sannan ya ce to insha Allah. Na sani cewa, Shaikh Adamu Tsoho kan bani lokaci ta yadda za mu shafe awa daya ko biyu muna magana, wanda a cikinta akwai karantarwa da tarbiya, ba zai taba nuna min ya gaji ba, sai in ni ne nace Abbah bari in je. Sai yace to insha Allah. Kuma na ga yadda yake ma duk mutane hakan, babba kake ko karamin yaro. 


Saboda saukin halinsa da jin cewa shi ba komai ba ne, a cikin shekaru goma zuwa yanzu, na shaidi lokacin da ya kan hau mashin, ko Keke-Napep, ya je uzuri a cikin gari, in ya zama lalura ta sa motarsa tana wajen gyara ko tana ajiye a lalace. Kuma ina tsammanin a 2020 ne, muna hanyar zuwa Sakkwato da shi, don Zikiran Shahadar Malam Qasim Umar, mota ta lalace mana a hanyar Zariya bayan mun bar Pambegua, yace mu barwa Khalid (Haris) da Maigoro (Driver) motar a gyara ta, ya cire rawani da abaya, muka hau motar haya, muka karisa Zariya, aka kuma samun motar haya, muka hau ta zuwa Sakkwato, muka isa wajajen karfe 12 na dare.


Bai fi 'yan watanni ba, haka ta taba maimaituwa, inda mota ta baci musu a gab da Saminaka, sai motar haya ya hau ya zo Unguwar Bawa, a daren, aka samu motar haya ya hau tare da sauran fasinja ya karisa gida Jos. A yayin da a mafi yawan lokuta shi kadai yake tuka mota ya je unguwa, ziyara, gaisuwa ko kasuwa a cikin garin Jos. Ba ma haka ba, ko ana gobe rasuwarsa, mutanen unguwarsa da dama sun shaida cewa sun ganshi da safe rike da hannun Ɗan autansa Abul Fadl Abbas, da jikansa mai shekaru shida, Muhammad, suna takawa su uku a kasa sun je shago a saman sun sayi abu sun dawo. 


Ya rayu a talaka, wanda ko gidan kansa bai mallaka ba, har Allah Ya masa rasuwa yana rayuwa ne a gidan aro, amma haka bai hana shi duk sadda wani ya zo masa da bukata ya nemi yadda zai yi ko da ta hanyar cin bashi ne, ya biya masa ba. Hatta a satin da zai rasu, sai da wani ya zo masa da koken kudin haya, za a tashe shi a gida akan dubu 100, Shaikh Adamu Tsoho ya turawa wasu matasa koken, tare da boye wane ne mutumin, da aka sallami mutumin, shi da kansa ya nemi wadanda suka yin yana musu godiya. Wanda yake nufin ya boye musu wane ne mai bukata don ya rufa masa asiri, ya kuma bayyana wa mai bukata cewa ga wadanda suka yi, don kar ya dauka shi ne ya yi.


Wani ikon Allah shi ne, shi ya rasu, bai da ko Naira dubu ɗarin a Asusun bankinsa, kuma bai da ko Naira dubu biyar a aljihun rigarsa ko a dakinsa. A haka, ya rika daukan dawainiyar marayu da dama, ta fuskacin karatunsu, da ma hidindimun rayuwa. Ya rike wasu a matsayin ya'yansa ta yadda hatta dinkin sallah, da abinci, da sauran bukatun rayuwa shi ke musu. Wasu kuma suna gaban iyayensu, musamman yan uwa na addini, da na zumunci da makwafta, bai taba ganin wani yaro na neman fasa karatu saboda kasawar iyayensa, face ya yi iyakan kokarinsa wajen ganin ya nemo yadda zai cigaba ba.


Mafi yawan gidajen da ke kewaye da shi Ahlussunnah ne, ko in ce tan Izala ne, Amma kaf din yaran unguwan da matasan unguwa, Abbah suke kiransa, a iya sanina ni ban san mai raina shi a cikin makwaftansa ba, saboda yadda yake mu'amala da mutanen unguwar, wanda ta kai ga har yakan fita ya bi jam'in sallah a masallacin unguwan wanda yake na Ahlussunnah ne. Ko da ya rasu, wani yana ce mana, ba jiya da Asubah a nan masallacinmu ya yi sallah ba?


Haka yasa, ko a shekarar 2016 da soja suka kona Markaz din Jos, suka kama mutane kusan 40 suka harbi wasu suka tafi da su, sun gangaro suka rika harba Tiyagas a gidan Shaikh Adamu Tsoho, da nufin su kutsa su kamo shi, su kona gidan, amma wallahi 'yan unguwar ne suka fito suka ce basu yarda ba, har sojin nan suka hakura, har ta kai ga Shaikh ya fita. Hatta ni da na je gidan da yamma a rannan, tare da abokina Ahmad Umar Dantala, DPO din unguwar rogo ya gangaro da mota da 'yan sanda da yan banga, suka kama ni a lokaci, mutanen unguwar suka taso suka ce ko su sake ni ko su kona motarsu, dole suka sake ni. 'Yan unguwar sun yi haka saboda sun sanni da Abbah. Ina son nuna muku ba kawai Malam din ba, tasirinsa ya kai ga makwaftansa su dauki kasada saboda wani nashi. 


Mutanen garin Jos, kowa ya ganka a kwanakin rasuwar Shaikh Adamu Tsoho, in dai ya ganka da alamin juyayi, kamar bakin kaya, za ka ji yace maka ya hakurin Malam? Bai fada da kowa, bai zagin kowa, bai aibata kowa, bai shiga harkar kowa, don haka kowa na girmama shi. Ban san bangaren al'umman da bai zo Ta'aziyyar Shaikh Adamu Tsoho ba, kama daga Wakilan Darikar Tijjaniyya da Qadiriyya, Izala, 'yan boko, 'yan siyasa, har Kiristoci da dukkan bangarorin al'umma, duk wanda ya zo cewa yake, an yi rashin mutumin kirki, mai hakuri, Malami nagari, mai zumunci.


Yana da juriya, duk tsawon shekarun Waki'ar Buhari, Shaikh Adamu Tsoho na fama da jinya, amma a haka yake duk kokarin da yake iya yi, na zagayen Mauludai, wanda sai ya yi mako biyu ko uku baya gida, kullum yana yawon wa'azi da tunatarwa, da fafutukan kira a saki Jagora a Abuja, wanda a mafi yawan lokaci bai da lafiya, bai da kudi, za a daddagara a samu ko da na man tafiya ne, a tafi, aje ana Muzahara ana hutawa ana komawa sahu, ba zai taba nunawa wani cikinsa ba. Za ka ganshi fes, ka dauka komai fes ne, har ma a samu masu neman tallafin kudin mota ko na abinci, kuma ko da bashi ne zai nema ya basu a asirce.


Yana da son taimako, ta yadda haka kawai yakan nemi asusun bankin gajiyayyu da tsofaffi, da mabukata, da ya samu wata dubu ashirin, za ka ga yana turawa mutane dubu biyar, dubu uku, dubu biyu. Haka ma Infaki, ko da yake jinyar nan a Iran wata guda da ya gabata, bayan an bude sabon asusun neman Infakin Cibiyar Wallafa, ya turo nasa na wata biyar, yace min, kafin lokacin zai cika na shekara in sun samu.


Mai karatu, wallahi baya ga Jagora (H), ni ban taba yin sallah a bayan wani in ji natsuwa kwatankwacin ace Jagora ke janmu, irin Shaikh Adamu Tsoho ba. Ya iya sallah sosai, za ka ji ta da dukkan natsuwa, kamar kar a kare. Ni shaida ne na tsayuwar darensa a halin tafiye-tafiye da kuma lokacin zaman gida. A yayin da gidan da ya rayu yake kuntataccen gaske, dakinsa na haɗe da barandan da yake zama da baki, duk yadda ya kai ga kasa da muryarsa da daddare kana iya jin duk motsinsa in yana ibada daga nan wajen.


Yana son yara sosai, yakan yawaita fitowa ya zauna a kujera a kofar gidansa dauke da littafin nazari da kuma ledan alawa, yara su zo su kewaye shi ya rika basu. A mafi yawan lokaci yakan share awa guda a wajen shi kadai, in ba an yi sa'a akwai wani a gidan, ko kuma ya zo a ranar da wasu Harisawa kan zo gidan don 'duty' ba. Kusan duk kananan yaran makwaftansa ya rike sunayensu, abin da kan ma mutane da dama wahala a yanzu.


Ya gama Mahaifiyarsa lafiya, ya mata janaza da kansa. Mahaifinsa kuwa da bai fi shekara biyu da rasuwa ba, da kansa yace wa Shaikh Adamu; Malam, ina son in riga ka rasuwa, saboda ka min janaza irin yadda ka wa mahaifiyarka. Kuma haka ta kasance, duk kuwa da shi da ne na hudu a wajen mahaifin nasu amma shi ya kasance babban gidan. Sannan bai watsar da zumunci ba, yanzu duk yan uwansa sun zama marayu da rashin Shaikh Adamu Tsoho, kusan fiye da lokacin rasuwar mahaifansu.


Tun bayan rasuwar mahaifina, yau shekara kusan 11 kenan, Shaikh Adamu Tsoho ya mai da ni dansa, ta fuskacin kowace irin kulawa, musamman bangaren ilimi da tarbiya da zumunci, har aka wayi gari wasu na dauka ko alakar jini ne a tsakaninmu da shi. Da yake mutum ne mai girmama mutane, har nakan ji nauyinsa akan yadda yake alakar girmamawa garemu a matsayin 'ya'yansa. Kuma haka ne, da rashinsa ne na fi tuna cewa ashe mahaifina ya rasu. Ƙarfina ya ragu, tsayuwata na neman ɓuya, Allah Ya min agajin tabbatarta. Wannan wanda duk sadda ya ga na yi ba daidai ba ko da a Social Media ne, daya daga sakonninsa na hikima gare ni shi ne; "A dage da aiki wajen taimakon su Malam (H) da duk abin da ake iyawa, haka muke fata daga gare ku. A guji shiga siyasar 'yan uwa, a kuma kaurace masa ko a rubutu, a yi kokari ya zama duk abin da ake yi ana yinsa ne saboda Allah, domin shi ne mai bayar da sakamako, a kuma yi kokarin kyautata alaka da Allah ta hanyar ibada, da nisantar haram, da koyi da tsarkakan bayi." ya tafi. 😭


Abbah, Allah Ya yafe gazawa da kurakuranka. Ya karbi kyawawan ayyukanka. Ya amfanar da al'umma da ilimin da ka wanzar, da mutanen da ka gina da ilimi da tarbiya. Ya albarkaci zuriyarka. Ya sanya ka cikin rahamarSa tare da tsarkakan bayinSa (AS). Allah Ya girmama ladan Jagora (H), da iyalanka da dukkan yan uwa akan rashinka. Ya sa mu koma gareShi muna kan turbar da kuka tafi kuka barmu a kai.


— Saifullahi M. Kabir 

6 Safar 1446 (11/8/2023)

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post