Mutanen Kidandan suna ta tserewa saboda 'yan fashin daji
Abun tausayi, mazauna garin Kidandan ta ƙaramar Hukumar Giwa jihar Kaduna kenan, maza da mata da ƙananan yara suke ƙauracewa mazauninsu, sakamakon kisa da fyaɗe da garkuwa da mutanen garin da ƴan ta'adda ke yi ba dare ba rana.
Mutanen wannan gari sun yi kiraye-kiraye a kan gwamnati ta taimaka musu a kan wannan kisan ƙare dangi da ƴan ta'adda ke musu a garin su da gonakinsu, amma babu wani taimako da gwamnati take musu a kan wannan matsala.
Sai ƴan ta'adda su shigo garin su shafe fiye da awa 10, babu soja ko ɗan sanda da ya kawo agaji.
Sun kashe musu mutane ba adadi, sun raunata su, sun yi satar dukiya mai ɗimbin yawa, sun yi garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa ba iyaka.
Wanda hakan ya yi sanadiyyar talaucewar manyan masu arzikin garin; duk wannan babu wani taimako da Gwamnati ke kawo wa wannan gari na Kidandan.
Shi ya sa mutanen garin da yawa suka yanke shawarar barin garin, wasu ma ba tare da sun san inda suka nufa ba. Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun!
Allah mun tuba, ka kawo mana ƙarshen wannan musiba da ke tafiya da rayukan ƴan uwan mu ba ƙaƙƙautawa 😭
9/8/2024
@Ma'asumah Nigerian News update
Daga shafin Yarima Bk Dtm