ZANYI KORAR BAKI DA BA A TABA YI BA A TARIHIN AMURKA - TRUMP

 


Zan yi korar baƙi da ba a taɓa yi ba a tarihin Amurka - Trump


Tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce idan ya sake zama shugaban kasar zai yi korar baki da ba a taba yi ba a tarihin kasar.


Trump ya fadi hakan ne yayin da yake gabatar da jawabin amincewa da takarar da jamiyyarsa ta Republican ta ba shi a zaben shugaban kasar da za a yi a watan Nuwamba, a wajen babban taron jam'iyyar da aka shiga rana ta hudu kuma ta karshe a Milwaukee.


Ya yi bayani kan yunkurin kashe shi da wani dan bindiga ya yi a ranar Asabar, inda ya bayyana irin halin da ya ce Amurka da duniya sun shiga bayan shugabancinsa tare kuma da irin matakan da zai dauka idan har ya sake dawo wa kan shugabancin a zaben da za a yi a watan Nuwamba.


Donald Trump wanda ya shafe sama da sa’a daya yana gabatar da jawabin nasa wanda galibi kusan da ka yai maimakon a ce jawabi ne a rubuce, ya fara ne da kiran neman hadin kai.


Shugaban ya ce yanzu lokaci ne na sauyi, kafin kuma daga bisani ya shiga gabatar da alkawura daban-daban ga Amurkawa.


A jawabin ya bayyana yadda ya tsallake rijiya da baya a yunkurin da wani dan bindiga ya yi na hallaka , inda ya ce, hankalinsa bai tashi ba, domin Allah yana tare da shi a.


Ya bayyana yadda ya ji lokacin da harsashin ya same shi a kunne;


''lokacin da na ji kara na ji wani abu ya buge ni, da karfi sosai a kunnena na dama. Sai na ce wa kaina, Kai mene ne wannan? Kai wannan harsashi ne kawai, na kai hannuna na dama wajen kunnena, na sauko da hannuna , hannuna duk jini.’’


Tsohon shugaban ya yi alkawarin rage hauhawar farashin kayayyaki da kawo karshen shiga kasar da bakin haure kanyi, inda ya yi alkawarin kammala ganuwar da ya fara wadda za ta raba Amurka da Mexico, inda bakin haure kan bi su shiga.shiga.


Ya ce zai kawo karshen shigar bakin haure nan take a ranar farko inda zai rufe iyakar.


@Ma'asumah Nigerian News update

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post