YEMEN TACE TANA MARABA DA YAKIN GABA DA GABA TSAKANIN TA DA HKI,
Shugaban kungiyar gwagwarmayar Ansarullah ta kasar Yemen ya gargadi Kasar tatsuniya cewa kasar Yemen na iya tunkarar ta fiye da yadda ake tsammani.
Yemen kuma ba zata kasawa ba wajen goyan bayan al’ummar falasdinu da ake zalinta inji shi.
Sayyed Abdul-Malik al-Houthi ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi a jiya Lahadi, kwana guda bayan da jiragen yakin haramtacciyar kasar tatsuniya suka kai hare-hare ta sama kan lardin Hudaidah mai matukar muhimmanci a Yemen, a matsayin ramuwar gayya kan harin da Yemen ta kai kan Tel-Aviv ranar Juma’a.
Shugaban kungiyar Ansarullah ya ce: “Al’ummar Yemen na maraba da duk wata irin arangama kai tsaye da makiya kasar tatsuniya yana mai jaddada cewa kasar tatsuniya ba za ta iya hana goyon bayan Yemen ga Gaza ba.
Al-Houthi ya kuma kara da cewa, hare-haren da haramtacciyar kasar tatsuniya ta kai kan Hudaidah “na nufin tattalin arzikin kasar Yemen ne,” yana mai cewa matakin da gwamnatin kasar ta dauka a birnin mai tashar jiragen ruwa ya tabbatar da cewa tana da nufin cutar da rayuwar Yemen din.
Shugaban kungiyar Ansurallah ya jaddada cewa, akwai bukatar a kara matsa lamba don tilastawa haramtacciyar kasar tatsuniya dakatar da mumunar ta’asar da take yi a zirin Gaza yayin da yakin ya shiga wata na goma.
Kalaman na baya-bayan nan sun zo ne bayan da ma’aikatar lafiya da jama’a ta Yemen ta ce adadin wadanda suka mutu sakamakon hare-haren da haramtacciyar kasar tatsuniya ta kai kan Hudaida ya kai 6.
@Ma'asumah Nigerian News update