Yadda farashin kaya ya riƙa tashi a wata shidan farko na 2024 a Najeriya
Farashin kayayyaki a Najeriya na ci gaba da hauhawa a watanni shida a jere na 2024.
A sabon rahoton da hukumar ƙididdiga ta Najeriya (NBS) ta fitar ya ce hauhawar farashi a ƙasar ta ƙaru zuwa kashi 34.19 cikin 100 a watan Yunin da ya gabata.
Kuma tsawon wata 18 a jere ke nan da ake samun hauhawar farashi a Najeriya, duk da matakan da hukumomin ƙasar ke ɗauka.
Hauhawar ta fi shafar kayan abinci inda sabbin alƙalumman na hukuma suka ce ya kai kashi 40.87 a watan Yunin 2024 idan aka kwatanta da Yunin 2023 inda aka samu ƙaruwar kaso 15.6
Tun a Janairun 2024, hukumar samar da abinci ta duniya FAO ta yi gargaɗin cewa za a fuskanci hauhawar farashin kayan abinci a Najeriya da sauran ƙasashen Afirka ta yamma a shekarar 2024.
Kodayake, a wani hasashe na Asusun Lamuni na Duniya IMF a watan Mayu ya ce za a samu raguwar hauhawar farashin kaya a ƙasar a ƙarshen shekara, duk da cewa wasu na ganin matakan da ake ɗauka ba su nuna alamun samun rangwamen ba.
@ma'asumah Nigerian News update