YADDA AKE GANE MUTUM MAI HANKALI NE !!!
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
Sau da yawa ana samun mutane da kake gani kamar masu hankali ne amma a zahari basu da alkali, ko da kuwa suna aiki irin na masu hankali a ido.
Siffantuwar da mutum ke yi shi ke nuna shi wanene, kana iya gane mai hankali ne ko akasin haka.
Imam Ali (A. S) na cewa
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
قال الإمام علي بن أبي طالب(ع):
" شِيمَةُ ذَوِي الْأَلْبَابِ وَالنُّهَى الْإِقْبَالُ عَلَى دَارِ الْبَقَاءِ وَالْإِعْرَاضُ عَنْ دَارِ الْفَنَاءِ وَالتَّوَلُّهُ بِجَنَّةِ الْمَأْوَى."
" SIFFOFIN MASU HANKALI DA HANGEN NESA SHINE FUSKANTUWA AKAN GIDA MAI WANZUWA (lahira), DA KAU DA KAI DAGA GIDA MAI QAREWA (duniya), DA KUMA JUYAWARSA GA ALJANNAR MAKOMA ."
المصدر : غرر الحكم ودرر الكلم
A wata riwaya kuma yake cewa :
" مَنْ عَمَّرَ دَارَ إِقَامَتِهِ فَهُوَ الْعَاقِلُ."
" WANDA KE RAYA GIDAN DAWWAMA SHINE MAI HANKALI. "
المصدر : غرر الحكم ودرر الكلم
Darasin da wannan hadisi ke karantarwa shine, shi mai hankali a ko-da-yaushe tunaninsa shine fifita gidan da ba ya qarewa da kuma kusantar gidan da yake fatan shigarsa wanda ba a nadama cikinsa.
Shi kuwa marar hankali da hangen nesa shine mai fifita gidan da ake barinsa, wato wanda ba a dawwama cikinsa.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.
22nd July, 2024/ 15th Muharram, 1445.