SOJOJIN YAMEN SUN FITAR DA HOTUNAN JIRGI MARAS MATUKA MAI SUNA SUNA "YAAFA',


sashen yada labaran yaki na sojojin kasar Yemen a ranar (Talata) ya watsa wani faifan bidiyo na lokacin da aka harba jirgi maras matuki na "Yaafa" zuwa birnin Tel Aviv da kuma sashe na wuraren da aka bude na bajakolin na musamman na wannan jirgi maras matuki tare da wasu fasalolinsa.


A cewar wannan rahoto, jirgin Yafa maras matuki mai dogon zango wanda ya ke gudanar da aiki da yawa kuma yana iya daukar wadansu manyan makamai na yaki.


A baya-bayan nan ne sojojin kasar Yamen suka kai hari a wani ginin da ke tsakiyar birnin Tel Aviv ta hanyar amfani da wannan jirgin mara matuki, ya samu nasarar cimma manufarsa ta hanyar ratsa dukkan tsare-tsare da na’urorin kariya na gwamnatin sahyoniyawan da kuma tafiyar a sama da kilomita 2000.


An fitar da wadannan hotuna ne bayan da sojojin Yaman suka kai hari a tsakiyar birnin Tel Aviv da wani jirgin sama mara matuki a ranar Juma'a 19 ga watan Yuli. A yammacin ranar Asabar 20 ga watan Yulin shekara ta 2024 mayakan yahudawan sahyoniya sun kai hari kan tashar jiragen ruwa ta Al-Hudaida da ke yammacin kasar Yemen. Dangane da haka ne ma'aikatar lafiya ta kasar Yemen ta sanar da cewa 'yan kasar Yemen 6 ne suka yi shahada, kuma 3 sun bace, yayin da wasu 83 suka jikkata a wannan hari.


Dangane da haka, Birgediya Janar Yahya Saree kakakin rundunar sojin Yaman ya jaddada cewa mayar da martani kan wannan aika-aika zai kasance tabbataccen abu da babu makawa, harin martanin zai kasance babba kuma mai zafi ga sahyoniyawan. Ya sanar da cewa sojojin kasar Yemen suna da wani hadafi na hari a Palastinu da ke mamaye da za su kai wa hari, wadanda suka hada da sansanonin soji da tsaro na gwamnatin yahudawan sahyoniya, kuma za su ci gaba da kai hare-hare kan wadannan sansanonin domin mayar da martani ga kashe-kashe da laifukan yau da kullum na wannan gwamnati a zirin Gaza.

@-Ma'asumah Nigerian News update

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post