SOJOJIN HKI SUN KUTSA CIKIN YANKUNA DA DAMA A YAMMA DA KOGIN JORDAN,
Sojojin HKI sun kutsa cikin yankuna da dama a yankin yamma da kogin Jordan a safiyar Jiya Asabar, inda suka gamu da turjiya daga dakarun Falasdinawa wadanda suke kokarinn maida su.
Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa sojojin yahudawan sun kama dan jirida guda a garin Jaba’a da ke kusa da sansanin yan gudun hijira na Jenin a yayinda suka kai bafalasdine guda ga shahada a yannkin Khalil.
Wasu kafafen yada labarai na sada zumunta wato Internet sun bayyana cewa shahidin shi ne Ibrahin Za’aaqiq, dan shekara 20 a duniya kuma ya taba zaman kaso a hannun yahudawan, amma a safiyar Jiya Asabar ya yi shahada sanadiyyar albarsan da sojojin yahudawan da suka sami shi a cikin gida.
Labarin ya kammala da cewa Ibrahim bai fi makonni biyu da fita daga gidan yari ba ya hadu da ajalinsa a hannun sojojin yahudawan a safiyar jiya.
A Zirin Gaza kuma, a wasu sabbin hare haren da sojojin HKI suka kai da jiragen yaki a Nusairat sun kashe Falasdinawa akalla 24. Labarin ya kara da cewa, a gida guda a garin Nusairat sojojin yahudawan sun kasashe mutane 8. Banda haka hare haren sun kai garin Gaza da kuma Jabalia duk a zirin Gaza.
@Ma'asumah Nigerian News update