SAHABBAI DA ƳAƳAN SAHABBAI NE SUKA KASHE SAHABI IMAN HUSAIN (A.S) A KARBALA
Ko kun san akwai Sahabban Annabi (saww) dayawa a cikin waɗanda suka zo kashe Imam Husaini (a.s) kamar yanda akwai wasu Sahabban Annabi (saww) cikin mataimaka Imam Husain da suka yi shahada tare da shi ?
Na'am , babu shakka wannan magana haka take kuma babu mai musata sai wanda ya jahilci tarihi ko mutum mai tsananin musu da son jayayya , tabbas akwai wasu daga wanda suka yi tarayya cikin zuwa kashe Imam ya (a.s) da suka kasance Sahabban kakansa Annabi (saww) irin su Khalid bin Arɗafagul Azriy da Abdul Rahman bin Abi Sabrata.
Wannan kaɗai ya isa ya rusa batun nan na "Kulluhum Idulun" wai duk Sahabbai adilai ne , ina batun adalci da daraja ga mutumin da yayi tarayya cikin makasan Imam Husain (a.s) ?
Me yasa ba'a bayyana sunayen waɗannan Sahabban da suka yi tarayya cikin kashe Imam Husaini (a.s) ?
In sun yarda duk wanda ya kashe Imam Husaini (a.s) tsinanne ne kenan suma waɗannan Sahabban tsinannu ne ?
Masu cewa yan Shi'a ne suka kashe Imam Husaini (a.s) shin shima sahabi Abdul Rahman bin Abi Sabrata ɗan Shi'a ne ?
A takaice dai a Karbala Sahabbai da ƴaƴan Sahabbai ne suka kashe wasu Sahabbai irin su Imam Husaini (a.s) , to ina batun duk Sahabbai adilai ne mutanen kirki ?
@Ma'sumah Nigerian News update