RUNDUNAR ALLAH TAYI LUGUDEN WUTA KAN SOJOJIN HKI A SANSANIN SU,

 


RUNDUNAR ALLAH TAYI LUGUDEN WUTA KAN SOJOJIN HKI A SANSANIN SU,


Dakarun kungiyar Rundunar Allah ta kasar Lebanon ta bada sanarwan yin luguden wuta da makamai masu linzami kan taron sojojin HKI a sansaninsu da ke  ‘Mitaat’,a arewacin kasar Falasdinu da suka mamaye,  inda ta halaka ko ta raunata da dama daga cikinsu.


Bayanan da kungiyar ta fitar a safiyar Jiya Asabar, sun tabbatar da cewa makaman kungiyar sun fada kan sojojin ba tare da wani kuskure ba.


Bayanin ya kara da cewa kungiyar ta kai wadannan hare hare ne don tallafawa falasdinawa wadanda suke fafatawa da sojojin HKI a Gaza, da kuma saboda hare haren da take kaiwa a kudancin kasar Lebanon.


Kafafen yada labarai na HKI sun tabbatar da faduwar makamai masu linzami a kan garin Jalali daga yamma, ba tare da an ji jiniyar hatsari ta yi kara ba.


Sannan sojojin HKI sun ci gaba da kai hare hare kan kudancin kasar Lebanon, inda suka cilla makamai kan wata mota dauke da mutane biyu, suka kuma kaisu ga shahada.


Daga ranar 8 ga watan Octoban shekarar da ta gabata zuwa yanzu mutane 76 suka yi shahada a kudancin kasar Lebanon.

@Ma'asumah Nigerian News update

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post