RUNDUNAR Al-QASSAM TA LASHI TAKOBIN FATATTAKAR SOJOJIN MAMAYA A GAZA,
Kakakin rundunar sojin Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar Hamas ya jaddada cewa: Za su ci gaba da gangami da yaki har sai sun fatattaki ‘yan mamaya,
Kakakin rundunar sojin Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas Abu Hamza ya tabbatar da cewa: ‘Yan gwagwarmaya sun yi nasarar raunana karfin sojojin haramtacciyar kasar tatsuniya a yankin Shuja’iya da ke arewacin Gaza.
A cikin wani jawabi da kakakin rundunar sojin Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas Abu Hamza ya fitar ya jaddada cewa: Makircin makiya ya yi rauni a Rafah, musamman a unguwannin Shaboura, Yabna da Tal al-Sultan, inda suka yi ruwan makamai masu linzami kan tankokin yakin sojojin yahudawan sahayoniyya ‘yan ta’adda. Ya kara da cewa: ‘Yan gwagwarmaya suna nan a kowane fage tare da kawo cikas ga sojojin mamaya a dukkan yankuna.
Abu Hamza ya kuma yi Allah wadai da tsarin cin zarafin fursunonin Falasdinu a gidajen yarin haramtacciyar kasar Isra’ila, wanda ke nuni da dabbanci na ‘yan sahayoniyya zaluncinsu, yana mai bayyana cewa; Gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar tatsuniya tana take hakkokin fursunonin da suke tsare a gidajen yarinta ta mummunar hanyar da ba a taba gani ba.
@Ma'asumah Nigerian News update