MAYAKAN YEMEN SUN KAI HARI BIRNIN TAL-AVIV NA KASAR TATSUNIYA,
Dakarun kasar Yemen, sun dauki alhakin kai wani hari da jirgi marar matuki da ya yi sanadin mutuwar mutum guda da raunata wasu akalla goma a birnin Tel-Aviv.
Kakakin rundunar sojin Yemen Yahya Saree ya ce: Mun kai hari a Tel Aviv da sabon jirgin mara matuki na “Jaffa”.
M. Saree ya jaddada a cikin wannan bayani cewa an kai wannan hari ne a matsayin mayar da martani ga kisan gillar da Ƙasar Tatsuniya ke yi wa ‘yan uwanmu a Gaza.
Sanarwar ta ce, an kai wannan harin ne da wani sabon jirgi mara matuki mai suna “Jaffa” wanda zai iya ratsawa ba tare da na’urori na radars sun iya gano shi ba.
An fitar da wannan sanarwa ne bayan da sojojin Haramtacciyar Ƙasar Tatsuniya suka sanar a yau cewa harin da aka kai a kusa da ofishin jakadancin Amurka a Tel Aviv ya haifar da fashewar wani abu.
Kafofin watsa labaran gwamnatin Ƙasar Tatsuniya ta ruwaito cewa “wani jirgi mara matuki makare da bama-bamai ya sake su a mahadar ababen hawa ta Shalom Aleichem da Ben Yehuda Streets da ke Tel Aviv, a daruruwan mitoci daga Ofishin Jakadancin Amurka.
Kakakin rundunar sojin Ƙasar Tatsuniya ya ce “bama-baman sun fashe ne da sanyin safiyar Juma’a a Tel Aviv sakamakon harin da aka kawo ta sama.” Kuma “Harin bai sa jiniya ta yi kara ba.
Wani gidan talbijin a kasar tatsuniya Channel 13 ya ambato wani rahoton wucin-gadi na soji da ke cewa an hango jirgin mara matuki da ya kai hari Tel Aviv amma an gaza kakkabo shi sakamakon “wani kuskure na dan’adam,” ba tare da yin cikakken bayani ba.
@ma'asumah Nigerian News update