JAGORA YAYI ALKAWARIN DAUKAR FANSAR JININ ISMAIL HANIYA,
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gargadi gwamnatin haramtacciyar kasar tatsuniya kan matakin mayar da martani mai tsauri kan kisan gillar da ta yi wa shugaban bangaren hukumar siyasa ta Hamas Ismail Haniyyah, yana mai cewa wajibi ne Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta dauki fansa kan jinin jagoran gwagwarmayar Palasdinawa.
Ayatullah Khamenei ya bayyana hakan ne sa’o’i bayan shahadar Haniya da ya isa birnin Tehran, don halartar bikin rantsar da sabon shugaban kasar Iran, wanda ya yi shahada a wani harin da kasar tatsuniya ta kai a kan masaukinsa.
Jagoran ya ce “Masu aikata laifuka ‘yan ta’adda yahudawan sahyoniya sun yi sanadin shahadar babban bakonmu a kasarmu ta haihuwa, kuma suka bar mu da bakin cikin hakan, amma kuma ta hanyar yin hakan kasar tatsuniya ta bude wani sabon shafin azabtar da kanta,” in ji Jagoran.
Ayatullah Khamenei ya yaba da sadaukarwar da Haniyyah ya kwashe tsawon shekaru yana yi a yakin da yake yi da mamayar kasar tatsuniya, yana mai cewa , da ma can Haniya a shirye yake ya yi shahada tare da sadaukar da ‘ya’yansa da iyalansa kan wannan tafarki.
Jagoran ya ci gaba da cewa: “Haniya Bai taba jin tsoron yin shahada a tafarkin Allah ba, amma mu kuma mun sha alwashin daukar fansa a kan jininsa a cikin wannan mummunan lamari da ya faru a yankin Jamhuriyar Musulunci.”
Jagoran ya kuma mika ta’aziyyarsa ga al’ummar musulmi, fa Falastinawa ‘yan gwagwarmaya, da sauran al’ummar Palastinu baki daya, da kuma iyalan Haniyyah, da iyalan daya daga cikin abokan tafiyarsa da ya yi shahada tare da shi.
@Ma'asumah Nigerian News update