IRAN TAYI MARABA DA SASANTAWAR KUNGIYOYIN FALASDINAWA,

 IRAN TAYI MARABA DA SASANTAWAR KUNGIYOYIN FALASDINAWA,



Gwamnatin kasar Iran ta yi maraba da sasantawa tsakanin kungiyoyin Falasdinawa da kuma hadin kansu wanda ya faru a birnin Beijing na kasar China a ranar Talatan da ta gabata.


Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Naseer Kan’ani ne ya bayyana haka a cikin shafinsa na X a safiyar yau Jumma’a, ya kuma kara da cewa, JMI zata ci gaba da tallafawa al-ummar Falasdinu har zuwa lokacinda zata sami cikekken iyncinta daga hannun yahudawan sahyoniyya. Har kuma zuwa lokacinda za’a kafa kasar Falasdinu mai cikekken yenci, mai babban birni a birnin Qudus mai alfarma.


Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya kammala da cewa hadin kan Falasdinawa zai taimaka wajen samun nasara a kan HKI, don haka ya yabawa kasar China da wannan gagrumin aikin da ta yi na hada kan kungiyar Falasdinawa bayan tattaunawa mai zufi a tsakaninsu na kwanaki uku a birnin Beijing. 


Kungiyoyin falasdinawan sun sami baraka mai tsanani a tsakaninsu ne a shekara ta 2007. Bayan da aka gudanar da zabe a shekara ta 2006 sannan kungiyar Hamas ta lashe mafi yawan kujerun majalisar dokokin kasar, da kuma Isma’ila Haniya na kungiyar hamas ya zama Firai ministan kasar.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post