IRAN TACE HARIN DA KASAR YEMEN TA KAI KAN TEL-AVIV GARGADI NE,

 



IRAN TACE  HARIN DA KASAR YEMEN TA KAI KAN TEL-AVIV GARGADI NE,


Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran na kasar iran ya yi magana kan harin da Yemen ta kai a kan birnin Tel Aviv na haramtacciyar kasar tatsuniya,


Limamin da ya jagoranci sallar juma’a a birnin Tehran Hujjatul-Islam Sayyid Muhammad Hasan Abu-Turabi Fard ya bayyana cewa: Harin da jiragen saman yakin Yemen suka kai birnin Tel Aviv na haramtacciyar kasar tatsuniya hari ne ‘yan gwagwarmaya suka kai tsakiyar birnin yahudawan sahayoniyya TelAviv, kuma kusa da ofishin jakadancin Amurka, wani karin gargadi ne ga kawo karshen zaluncin yahudawan  Sahayoniyya kan al’ummar Gaza.


Haka nan Hujjatul-Islam Sayyid Muhammad Hassan Abu Turabi Fard ya jaddada cewa: Harin ‘yan gwagwarmayar Yemen suka kai da jirage marasa matuka ciki kan birnin Tel Aviv a safiyar Jiya Juma’a, jiragen sama ne da matasan Yemen suka kera da kansu.


Yana mai jaddada cewa: Matsayin al’ummar Gaza ya sake haifar da wani suna ga al’ummar musulmi, ya kuma kara da cewa: Tsohon fira ministan yahudawan sahayoniyya ya ce: A kullum ana kashe sojojin su a Gaza kuma gwamnatinsu ta karye tare da durkushewa kuma a halin yanzu ba ta da wani tasiri ko kima a idon yahudawa. 


Haka nan babban hafsan sojin yahudawan sahayoniyya mai murabus ya ce: An yi galaba a kan sojojin yahudawan sahayoniyya a yakin Gaza, kuma yahudawa suna fama da rashin kayan aiki, rashin dabarun yaki, karancin abinci da abubuwan bukatun yau da kullum.


@Ma'asumah Nigerian News update

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post