Manyan jami’an diflomasiyyar Iran da Bahrain sun cimma matsaya kan samar da hanyoyin da suka dace don fara tattaunawa tsakanin kasashen biyu domin nazarin yadda za a maido da huldar siyasa a tsakaninsu.
Bayan ganawar ministan harkokin wajen kasar Iran na rikon kwarya Ali Bagheri da ministan harkokin wajen kasar Bahrain Abdul Latif Al-Ziani a birnin Tehran, bangarorin biyu sun fitar da sanarwar hadin gwiwa tare da cimma matsaya kan daukar matakan maido da alaka.
Tun da farko, a ganawa daban-daban da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da firaministan kasar Sin Li Qiang suka yi da Sarkin Bahrain Hamad bin Isa Al Khalifa, sarkin ya bayyana bukatar kasarsa kan maido da hulda da Tehran, kuma Iran ta yi maraba da wannan matsayi.
A cikin wannan bayani na hadin gwiwa, an bayyana cewa, akwai babban tsari na dangataka ta tarihi tsakanin masarautar Bahrain da Jamhuriyar Musulunci ta Iran da alaka ta addini, makwabtaka, tarihi da maslahar juna a tsakaninsu”,
A wannan ganawar, bangarorin biyu sun amince da samar da hanyoyin da suka dace don fara tattaunawa tsakanin kasashen biyu, domin nazarin yadda za a maido da huldar siyasa a tsakanin kasashensu ba tare da wani bata lokaci ba.
Bbn Suhaila
@Ma'asumahNigareanNewsUpdate