Guterres Ya Nuna Matukar Damuwa Game Da Harin Isra’ila Kan Yemen,
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guteress, ya nuna matukar damuwa game da harin da Isra’ila ta kai a lardin Hodeidah na kasar Yemen.
Mista Guterres, ya bayyana matukar damuwarsa kan hare-haren Isra’ila a tashar ruwan Hodeidah da ke Yeman, a cewar wata sanarwa da aka aike wa ‘yan jarida.
“Sakataren Janar ya yi kira ga duk wanda abin ya shafa da su guji kai hare-hare da ka iya cutar da fararen hula da kuma lalata ababen more rayuwa na farar hula.
@ Ma'asumah Nigerian News update
Tags:
Kasashen Waje