EDIL GHADIR YAFI KOWANI EDI A GURIN ALLAH (SWT)




Allah(swt) yana cewa:


"Ya kai Annabi(saw)! isar da abinda Allah ya aiko maka; idan ba ka isar ba tamkar ba ka isar da sako ba; tabbas! Allah zai kiyayeka daga mutane" (Q : 5 : 67):


 ﻳَٰٓﺄَﻳُّﻬَﺎ ﭐﻟﺮَّﺳُﻮﻝُ ﺑَﻠِّﻎۡ ﻣَﺎٓ ﺃُﻧﺰِﻝَ ﺇِﻟَﻴۡﻚَ ﻣِﻦ ﺭَّﺑِّﻚَۖ ﻭَﺇِﻥ ﻟَّﻢۡ ﺗَﻔۡﻌَﻞۡ ﻓَﻤَﺎ ﺑَﻠَّﻐۡﺖَ ﺭِﺳَﺎﻟَﺘَﻪُۥۚ ﻭَﭐﻟﻠَّﻪُ ﻳَﻌۡﺼِﻤُﻚَ ﻣِﻦَ ﭐﻟﻨَّﺎﺱِۗ ﺇِﻥَّ ﭐﻟﻠَّﻪَ ﻟَﺎ ﻳَﻬۡﺪِﻱ ﭐﻟۡﻘَﻮۡﻡَ ﭐﻟۡﻜَٰﻔِﺮِﻳﻦَ


(Al-Ma'ida : 67).


Manyan malaman da Ahlus-Sunnah a fagen Tafsiri, Hadisi da Asbabun-Nuzul...; sun tabbatar da cewa wannan ayar ta sauka ne daf da al'amarin Ghadir, kuma bayan Mala'ika Jibril(as) ya sauko da wannan ayar ne Annabi(saw) ya tara Sahabbansa a Ghadir Khum ya shelanta cewa Imam Ali(as) ne khalifa a bayansa:


Fakhrud-Deen Ar-Razi (Babban malamin Ahlus-sunnah) ya tabbatar da cewa; Ayar isar da sako (Ayatut-Tablig) ta sauka ne daf da al'amarin Ghadir, kuma bayan Mala'ika Jibril(as) ya sauko da wannan ayar ne Annabi(saw) ya tara Sahabbansa a Ghadir Khum ya shelanta cewa Imam Ali(as) ne maula (Shugaba / Khalifa) a bayansa:


قال فخر الدين اﻟﺮاﺯﻱ:


ﻧﺰﻟﺖ اﻵﻳﺔ (ﻳﺎ ﺃﻳﻬﺎ اﻟﺮﺳﻮﻝ ﺑﻠﻎ ﻣﺎ ﺃﻧﺰﻝ ﺇﻟﻴﻚ ﻣﻦ ﺭﺑﻚ) ﻓﻲ ﻓﻀﻞ ﻋﻠﻲ ﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﻃﺎﻟﺐ(ع)، ﻭﻟﻤﺎ ﻧﺰﻟﺖ ﻫﺬﻩ اﻵﻳﺔ ﺃﺧﺬ ﺑﻴﺪﻩ ﻭﻗﺎﻝ: "ﻣﻦ ﻛﻨﺖ ﻣﻮﻻﻩ ﻓﻌﻠﻲ ﻣﻮﻻﻩ اﻟﻠﻬﻢ ﻭاﻝ ﻣﻦ ﻭاﻻﻩ ﻭﻋﺎﺩ ﻣﻦ ﻋﺎﺩاﻩ". ﻓﻠﻘﻴﻪ ﻋﻤﺮ(ر) ﻓﻘﺎﻝ: ﻫﻨﻴﺌﺎ ﻟﻚ ﻳﺎ اﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﻃﺎﻟﺐ ﺃﺻﺒﺤﺖ ﻣﻮﻻﻱ ﻭﻣﻮﻟﻰ ﻛﻞ ﻣﺆﻣﻦ ﻭﻣﺆﻣﻨﺔ، ﻭﻫﻮ ﻗﻮﻝ اﺑﻦ ﻋﺒﺎﺱ ﻭاﻟﺒﺮاء ﺑﻦ ﻋﺎﺯﺏ ﻭﻣﺤﻤﺪ ﺑﻦ ﻋﻠﻲ.


- ﺗﻔﺴﻴﺮ اﻟﺮاﺯﻱ = ﻣﻔﺎﺗﻴﺢ اﻟﻐﻴﺐ ﺃﻭ اﻟﺘﻔﺴﻴﺮ اﻟﻜﺒﻴﺮ-اﻟﺠﺰء اﻟﺜﺎﻧﻲ ﻋﺸﺮ - [ﺳﻮﺭﺓ اﻟﻤﺎﺋﺪﺓ (5) : ﺁﻳﺔ 68] - ﺻﻔﺤﺔ -401.


Jalalud-Deen As-Suyuti (Babban malamin Ahlus-sunnah) ya riwaito cewa; Ayar isar da sako (Ayatut-Tablig) ta sauka ne daf da al'amarin Ghadir, kuma bayan Mala'ika Jibril(as) ya sauko da wannan ayar ne Annabi(saw) ya tara Sahabbansa a Ghadir Khum ya shelanta cewa Imam Ali(as) ne maula (Shugaba / Khalifa) a bayansa:


قال جلال الدين السيوطي:


وأخرج ابن أبي حاتم وابن مردويه وابن عساكر عن أبي سعيد الخدري قال نزلت هذه الآية يا أيها الرسول بلغ ما أنزل إليك من ربك على رسول الله(ص) يوم غدير خم في علي بن أبي طالب.


وأخرج ابن مردويه عن ابن مسعود قال كنا نقرأ على عهد رسول الله(ص) يا أيها لرسول بلغ ما أنزل إليك من ربك ان عليا مولى المؤمنين وان لم تفعل فما بلغت رسالته والله يعصمك من الناس.


- الدر المنثور : جلال الدين السيوطي. الجزء : ٢، ص ٢٩٨. تاريخ الوفاة : ٩١١.


Tabbas ابن مردويه (Babban malamin Ahlus-sunnah) ya riwaito hadisai fiye da 5 da Isnadai daban-daban, akan cewa; Ayar isar da sako (Ayatut-Tablig) ta sauka ne daf da al'amarin Ghadir, kuma bayan Mala'ika Jibril(as) ya sauko da wannan ayar ne Annabi(saw) ya tara Sahabbansa a Ghadir Khum ya shelanta cewa Imam Ali(as) ne maula (Shugaba / Khalifa) a bayansa:


قال ابن مردويه:


قوله تعالى: (يا أيها الرسول بلغ مآ أنزل إليك من ربك وإن لم تفعل فما بلغت رسالته والله يعصمك من الناس). [الآية: ٦٧].


٣٤٥. ابن مردويه، عن أبي سعيد الخدري، قال: نزلت هذه الآية: (يا أيها الرسول بلغ مآ أنزل إليك من ربك) على رسول الله(ص) يوم غدير خم في علي بن أبي طالب. (الدر المنثور، ج ٢، ٢٩٨. روح المعاني، ج ٤، ص١٧٢. أسباب النزول، ص ١٣٥، أرجح المطالب، ص ٥٦٧).


٣٤٦. ابن مردويه، عن ابن مسعود، قال: كنا نقرأ على عهد رسول الله(ص) (يا أيها الرسول بلغ مآ أنزل إليك من ربك - إن عليا مولى المؤمنين - وإن لم تفعل فما بلغت رسالته والله يعصمك من الناس). (روح المعاني، ج٦، ص ١٧٢. الدر المنثور، ج ٢، ٢٩٨).


٣٤٧. ابن مردويه، عن أبي الجارود، عن أبي حمزة قال: (يا أيها الرسول بلغ مآ أنزل إليك من ربك) نزلت في شأن الولاية. (توضيح الدلائل، ص ١٥٧).


٣٤٨. ابن مردويه، عن زيد بن علي، قال: لما جاء جبرئيل(ع) بأمر الولاية، ضاق النبي (صلى الله عليه وآله) بذلك ذرعا، وقال: "قومي حديثوا عهد بجاهلية"، فنزلت. (كشف الغمة، ج ١، ص ٣١٧).


٣٤٩. ابن مردويه، عن ابن عباس، قال: لما أمر الله رسوله(ص) أن يقوم بعلي(ع) فيقول له ما قال، فقال(ص): "يا رب، إن قومي حديثوا عهد بجاهلية"، ثم مضى بحجه، فلما أقبل راجعا نزل بغدير خم أنزل الله عليه: (يا أيها الرسول بلغ مآ أنزل إليك من ربك وإن لم تفعل فما بلغت رسالته) فأخذ بعضد علي، ثم خرج إلى الناس، فقال: " أيها الناس ألست أولى بكم من أنفسكم؟ "قالوا: بلى يا رسول الله. قال: "اللهم من كنت مولاه فعلي مولاه، اللهم وال من والاه وعاد من عاداه، وأعن من أعانه، واخذل من خذله، وانصر من نصره، وأحب من أحبه وابغض من أبغضه "، قال ابن عباس: فوجبت والله في رقاب القوم. وقال حسان بن ثابت: يناديهم يوم الغدير نبيهم * بخم واسمع بالرسول مناديا يقول: فمن مولاكم ووليكم؟ * فقالوا ولم يبدوا هناك التعاميا إلهك مولانا وأنت ولينا * ولم تر منا في الولاية عاصيا فقال له: قم يا علي، فإنني * رضيتك من بعدي إماما وهاديا.


- مناقب علي بن أبي طالب(ع) وما نزل من القرآن في علي(ع) : أبي بكر أحمد بن موسى ابن مردويه الأصفهاني، ص ١٣٩ - ٢٤١. تاريخ الوفاة : ٤١٠. تحقيق : جمعه ورتبه وقدم له : عبد الرزاق محمد حسين حرز الدين. الطبعة : الثانية. تاريخ النشر : ١٤٢٤ - ١٣٨٢ش.


Allamah Al-Alusi (Babban malamin Ahlus-sunnah) ya tabbatar da cewa; [yan Shia su na kafa hujja da Hadisai ingantattu da su ka riwaito daga Ahlul-bayt(as)] akan cewa; Ayar isar da sako (Ayatut-Tablig) ta sauka ne daf da al'amarin Ghadir, kuma bayan Mala'ika Jibril(as) ya sauko da wannan ayar ne Annabi(saw) ya tara Sahabbansa a Ghadir Khum ya shelanta cewa Imam Ali(as) ne maula (Shugaba / Khalifa) a bayansa.


Sai Al-Alusi ya kara da cewa:


Tabbas manyan malaman da Ahlus-Sunnah sun riwaito daga Abdullah Ibn Abbas, Abdullah Ibn Mas'ud... akan cewa; Ayar isar da sako (Ayatut-Tablig) ta sauka ne daf da al'amarin Ghadir, kuma bayan Mala'ika Jibril(as) ya sauko da wannan ayar ne Annabi(saw) ya tara Sahabbansa a Ghadir Khum ya shelanta cewa Imam Ali(as) ne khalifa a bayansa.


Al-amarin Khadir Khum shine babbar hujjar 'yan Shia akan tabbatar da cewa Imam Ali(as) ne Khalifan Annabi Muhammad(saw) na farko:


قال الآلوسي:


...أن المراد: ب (ما أنزل إليك) خلافة علي(ك)، فقد رووا بأسانيدهم عن أبي جعفر وأبي عبد الله(ر) أن الله تعالى أوحى إلى نبيه(ص) أن يستخلف عليا كرم الله تعالى وجهه، فكان يخاف أن يشق ذلك على جماعة من أصحابه فأنزل الله(ت) هذه الآية تشجيعا له(ع) بما أمره بأدائه.


وعن ابن عباس(ر) قال: نزلت هذه الآية في علي(ك) حيث أمر سبحانه أن يخبر الناس بولايته فتخوف رسول الله(ص) أن يقولوا حابى ابن عمه وأن يطعنوا في ذلك عليه، فأوحى الله تعالى إليه هذه الآية فقام بولايته يوم غدير خم، وأخذ بيده فقال(ع): من كنت مولاه فعلي مولاه اللهم وال من والاه وعاد من عاداه.


وأخرج الجلال السيوطي في "الدر المنثور" عن أبي حاتم وابن مردويه وابن عساكر راوين عن أبي سعيد الخدري قال: نزلت هذه الآية على رسول الله(ص) يوم غدير خم في علي بن أبي طالب(ك).


وأخرج ابن مردويه عن ابن مسعود قال: كنا نقرأ على عهد رسول الله(ص): (يا أيها الرسول بلغ ما أنزل إليك من ربك) إن عليا ولي المؤمنين (وإن لم تفعل فما بلغت رسالته).


وخبر الغدير عمدة أدلتهم على خلافة الأمير(ك).


- تفسير الآلوسي : الآلوسي. الجزء : ٦، ص ١٩٢ - ١٩٣. تاريخ الوفاة : ١٢٧٠.


Tabbas Malaman Shia sun riwaito Hadisai (ingantattu) daga Ahlul-bayt(as) akan cewa; Ayar isar da sako (Ayatut-Tablig) ta sauka ne daf da al'amarin Ghadir, kuma bayan Mala'ika Jibril(as) ya sauko da wannan ayar ne Annabi(saw) ya tara Sahabbansa a Ghadir Khum ya shelanta cewa Imam Ali(as) ne maula (Shugaba / Khalifa) a bayansa:


٢٩٢ - محمد بن الحسين وغيره عن سهل عن محمد بن عيسى ومحمد بن يحيى ومحمد ابن الحسين جميعا عن محمد بن سنان عن إسماعيل بن جابر وعبد الكريم بن عمرو عن عبد الحميد ابن أبي الديلم عن أبي عبد الله(ع) (حديث طويل، يقول فيه(ع): فلما رجع رسول الله(ص) من حجة الوداع نزل عليه جبرئيل(ع) فقال: (يا أيها الرسول بلغ ما انزل إليك من ربك وان لم تفعل فما بلغت رسالته والله يعصمك من الناس ان الله لا يهدى القوم الكافرين) فنادى الناس فاجتمعوا وامر بسمرات فقم شوكهن ثم قال(ص): يا أيها الناس من وليكم وأولى بكم من أنفسكم؟ فقالوا: الله ورسوله فقال: من كنت مولاه فعلى مولاه اللهم وال من والاه وعاد من عاداه ثلث مرات.


- تفسير نور الثقلين : الشيخ الحويزي، الجزء : ١، ص ٦٥٢ - ٦٥٣. تاريخ الوفاة : ١١١٢. تحقيق : تصحيح وتعليق : السيد هاشم الرسولي المحلاتي. الطبعة : الرابعة. تاريخ النشر : ١٤١٢ - ١٣٧٠ ش.


Ga karin wasu manyan malaman Ahlus-Sunnah da suka ambaci cewa; Ayar Isar da sako (Ayatut-Tablig) ta sauka akan tabbatar da Khalifancin Imam Ali(as), kaitsaye bayan wafatin Annabi Muhammad(saw):


1. Badruddin Hanafi, a Umdatul Qari Fi Sharh Sahih Bukhari, j; 8, s. 584.


2. Ali Bin Ahmad Wahidi, a Asbabun Nuzul, s. 150.


3. Muhammad Bin Talha Shafi'i, a Matalibus Su'ul, s. 16.


4. Hafiz Ibn Mardawiyya; Tafsirin Ayar.


5. Hafiz Abul Qasim Haskani; Shawahidut-Tanzil.


6. Abul Fatha Nazari a Khasa'isul Alawi.


7. Mu'inuddin Meibudi, a Sharh Diwan.


8. Qazi Shekani a Fathul Ghadir, j; III, s. 57; 


9. Seyyed Jamaluddin Shirazi, a Arba'in.


10. Hafiz Ibn Abi Hatim Razi, a littafinsa; 'Ghadir'.


11. Ahmad Tha'alabi, a  Tafsir Kashfu'l-Bayan.


12. Hafiz Abu Ja'afar Tabari, a Kitabul-Wilaya. 


13. Hafiz Abu Nu'aim Ispahani, a littafinsa; Ma nazala minal-Qur'an Fi Ali. 


14. Ibrahim Bin Muhammad Hamwaini a littafinsa; Fara'idus Simtain.


15. Nizamu'd-din Nishapuri, a Tafsir, j; VI, s. 170.


16. Hafiz Abu Sa'id Sijistani a Kitabul Wilaya. 


17. Nuruddin Bin Sabbagh Maliki a Fusulul Muhimma, s. 27.


18. Hafiz Abu Abdullah Mahamili, a Amali.

 

19. Hafiz Abubakar Shirazi, a Ma Nazala minal Qur'an Fi Amiril Mu'minin Ali(as).


20. Mir Seyyed Ali Hamadani Shafi'i, a Mawadda V, daga  Mawaddatul-Qurba.


21. Sheikh Sulayman Balkhi Hanafi, a Yanabiul Mawadda, babina 39.


A takaicce, fitattaun malaman Ahlus-Sunnah fiye da 30 ne suka rubuta a littafansu cewa wannan ayar ta sauka ne a Ghadir Khum, akan sha'anin nasabta Imam Ali(as) a matsayin khalifa bayan Annabi(saw).


Harma Qazi Fazl Bin Ruzbahan; shehin malamin Ahlus-Sunnah mai matukar ta'assubanci, yana cewa;


"Gaskiya ya inganta wannan ayar ta sauka ne a Ghadir, kuma ana saukar da wannan ayar Annabi(saw) ya daga hannun Imam Ali(as) ya ce; duk wanda na kasance shugabansa to Ali(as) shugabansa ne".


Wannan ayar ta na tabbatar mana cewa; Allah(swt) ya san cewa akwai wadanda za su yi adawa, suki yiwa Imam Ali(as) biyayya a bayan Annabi(saw), hakan ta sa a ayar Allah yace; "Allah zai kiyayeka (Annabi) daga mutane (wadanda ba sa son Imam Ali(as) ya zama khalifan Annabi(saw) na farko)" (Q : 5 : 67).


Shi kansa Annabi Muhammad(saw) ya san akwai 'yan adawa da kasancewa Imam Ali(as) a matsayin magajinsa, shiyasa ya ke jinkiri akan al'amarin, har sai da takai Allah(swt) ya saukar da wannan ayar, kuma Allah(stw) ya tabbatarwa Annabi(saw) cewa nasabta Imam Ali(as) a matsayin khalifa bayan Annabi(saw) cikamakon isar da manzanci ne; rashin yin hakan tamkar rasu manzanci ne kacokaf.


Wannan ne yasa a akidar Shia Imamiyyah; imamanci da Annabta usulai ne daga usuluddin; wato rusa daya daga cikinsu tamkar rusa addini ne kacokaf.


Ayoyin Qur'ani masu yawa su na tambatar haka, daga ciki har da Ayar 'Ikmaluddin' da Ayar 'Wilaya'...


Sani Muh'd Sani Muh'd

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post