DUK WANI KHALIFANCI DA BA NA AHLUL-BAYT(AS) BA; JUYIN MULKI NE (COUP D'ETAT / انقلاب). - A MAHANGAR HADISAI SAHIHAI DA AL-BANI, AL-ARNA'UT... SU KA INGANTA.



DUK KHALIFAN DA BAYA CIKIN AHLUL-BAYT(AS); KHALIFANCINSA DAIDAI YAKE DA SHUGABAN DA YA HAMBARAR DA HALATTACCEN SHUGABA (COUP D'ETAT / انقلاب):


QUR'ANI DA AHLUL-BAYT(AS) NE KHALIFOFIN ANNABI MUHAMMAD(SAW). DON HAKA, RIKO DA BIYAYYA GA QUR'ANI DA AHLUL-BAYT(AS) NE KADAI HANYAR TSIRA (صراط المستقيم):


AKWAI AYAR QUR'ANI KO HADISI INGANTACCE DA ANNABI MUHAMMAD(SAW) YA CE; ABUBAKAR, UMAR, USMAN... KHALIFOFINSA NE; KAMAR YANDA YA AYYANA AHLUL-BAYT(AS) A MATSAYIN KHALIFOFINSA(SAW)???


Nassi Sarihi (karara) Sahihi da yake tabbatar da Qur'ani da Ahlul-bayt(as) ne Annabi Muhammad(saw) ya bar mana; a matsayin khalifofinsa; ya zo a littattafan Ahlus-Sunnah masu yawan gaske (a littattafan Ahlus-Sunnah sama da 100).


Muslim a Sahihin littafinsa ya riwaito cewa; Annabi(saw) ya yiwa Sahabbai Khuduba a Ghadir Khum (gurin da Annabi(saw) ya nada Imam Ali(as) a matsayin khalifansa na farko), sannan sai Annabi(saw) ya ce; tabbas lokacin wafatina ya kusa, don haka na bar maku nauyaya (khalifofi) 2: Qur'ani... da Ahlul-Bayt(as). Ina maku nasiha kar ku yarda ku bar (riko da biyayya) ga Ahlul-Bayt(as)! (Annabi(saw) ya ta maimaita hakan har sau 3):


2408 ( 36 ) حَدَّثَنِي  زُهَيْرُ بْنُ حَرْبٍ ،  وَشُجَاعُ بْنُ مَخْلَدٍ، جَمِيعًا عَنِ  ابْنِ عُلَيَّةَ، قَالَ زُهَيْرٌ: حَدَّثَنَا  إِسْمَاعِيلُ بْنُ إِبْرَاهِيمَ، حَدَّثَنِي أَبُو حَيَّانَ، حَدَّثَنِي  يَزِيدُ بْنُ حَيَّانَ، قَالَ: انْطَلَقْتُ أَنَا وَحُصَيْنُ بْنُ سَبْرَةَ، وَعُمَرُ بْنُ مُسْلِمٍ إِلَى  زَيْدِ بْنِ أَرْقَمَ... قَالَ : قَامَ رَسُولُ اللَّهِ(ص) يَوْمًا فِينَا خَطِيبًا بِمَاءٍ يُدْعَى خُمًّا، بَيْنَ مَكَّةَ وَالْمَدِينَةِ، فَحَمِدَ اللَّهَ وَأَثْنَى عَلَيْهِ، وَوَعَظَ وَذَكَّرَ، ثُمَّ قَالَ: "أَمَّا بَعْدُ ؛ أَلَا أَيُّهَا النَّاسُ، فَإِنَّمَا أَنَا بَشَرٌ، يُوشِكُ أَنْ يَأْتِيَ رَسُولُ رَبِّي فَأُجِيبَ، وَأَنَا تَارِكٌ فِيكُمْ ثَقَلَيْنِ ؛ أَوَّلُهُمَا كِتَابُ اللَّهِ، فِيهِ الْهُدَى وَالنُّورُ، فَخُذُوا بِكِتَابِ اللَّهِ، وَاسْتَمْسِكُوا بِهِ"، فَحَثَّ عَلَى كِتَابِ اللَّهِ وَرَغَّبَ فِيهِ، ثُمَّ قَالَ : "وَأَهْلُ بَيْتِي، أُذَكِّرُكُمُ اللَّهَ فِي أَهْلِ بَيْتِي، أُذَكِّرُكُمُ اللَّهَ فِي أَهْلِ بَيْتِي، أُذَكِّرُكُمُ اللَّهَ فِي أَهْلِ بَيْتِي "...


- صحيح مسلم : كتاب : فضائل الصحابة(ر)  | باب : من فضائل علي بن أبي طالب(ر) : 2408 ( 37 )... 


- سنن الترمذي ( 3788 ).


- سنن الدارمي ( 3359 ).


- مسند أحمد ( 19265, 19313 ).


Hadisin nauyaya (khalifofi) 2 (As-Sakalaini), (Qur'ani da Ahlul-bayt(as); da Annabi(saw) ya bar mana ya zo da sigogi masu yawan gaske, baya ga sigar da tazo a Sahihi Muslim, akwai kuma wata sigar da Annabi(saw) karara ya tabbatar mana khalifofinsa a bayansa sune: Qur'ani da Ahlul-bayt(as):


ﺣﺪﻳﺚ ﺍﻟﺜﻘﻠﻴﻦ ﺑﺼﻴﻐﺔ "ﺇﻧﻲ ﺗﺎﺭﻙ ﻓﻴﻜﻢ ﺧﻠﻴﻔﺘﻴﻦ ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻋﺘﺮﺗﻲ ﺃﻫﻞ ﺑﻴﺘﻲ".


Al-bani ya inganta hadisin da Annabi(saw) ya ce;


"Na bar maku khalifofi 2: Littafin Allah (Qur'ani).... da Ahlul-bayt(as). (Qur'ani da Ahlul-bayt(as) ba zasu taba rabuwa ba; har su riski Annabi(saw) a Al-Jannah":


ﺇﻧﻲ ﺗﺎﺭﻙ ﻓﻴﻜﻢ ﺧﻠﻴﻔﺘﻴﻦ: ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ ﺣﺒﻞ ﻣﻤﺪﻭﺩ ﻣﺎ ﺑﻴﻦ ﺍﻟﺴﻤﺎﺀ ﻭ ﺍﻷﺭﺽ ﻭ ﻋﺘﺮﺗﻲ ﺃﻫﻞ ﺑﻴﺘﻲ ﻭ ﺇﻧﻬﻤﺎ ﻟﻦ ﻳﺘﻔﺮﻗﺎ ﺣﺘﻰ ﻳﺮﺩﺍ ﻋﻠﻲ ﺍﻟﺤﻮﺽ. ﻋﻦ ﺯﻳﺪ ﺑﻦ ﺛﺎﺑﺖ. 


ﻗﺎﻝ ﺍﻟﺸﻴﺦ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ: ‏(ﺻﺤﻴﺢ‏) ﺍﻧﻈﺮ ﺣﺪﻳﺚ ﺭﻗﻢ: 2457 ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ).


- ﺻﺤﻴﺢ ﻭﺿﻌﻴﻒ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ﺍﻟﺼﻐﻴﺮ ﻭﺯﻳﺎﺩﺗﻪ : ﻣﺤﻤﺪ ﻧﺎﺻﺮ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﺍﻟﻨﺎﺷﺮ: ﺍﻟﻤﻜﺘﺐ ﺍﻹﺳﻼﻣﻲ ﻋﺪﺩ ﺍﻷﺟﺰﺍﺀ: 1 - ‏( 1 / 423 ‏) ﺡ 4222. 


Limamin Ahlus-Sunnah wal Jama'a kuma shugaban mazhabar Hambaliyya; Ahmad bin Hambal, ya nakalto sahihiyar riwayar hadisus-Sakalain da sigar da Annabi(saw) ya ce; ya bar mana khalifofi 2: Qur'ani da Ahlul-bayt(as):


21578 حَدَّثَنَا  الْأَسْوَدُ بْنُ عَامِرٍ، حَدَّثَنَا  شَرِيكٌ، عَنِ  الرُّكَيْنِ، عَنِ  الْقَاسِمِ بْنِ حَسَّانَ، عَنْ  زَيْدِ بْنِ ثَابِتٍ  قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ(ص): "إِنِّي تَارِكٌ فِيكُمْ خَلِيفَتَيْنِ : كِتَابَ اللَّهِ، حَبْلٌ مَمْدُودٌ مَا بَيْنَ السَّمَاءِ وَالْأَرْضِ - أَوْ مَا بَيْنَ السَّمَاءِ إِلَى الْأَرْضِ - وَعِتْرَتِي، أَهْلَ بَيْتِي، وَإِنَّهُمَا لَنْ يَتَفَرَّقَا حَتَّى يَرِدَا عَلَيَّ الْحَوْضَ ". 


- مسند أحمد : مسند الأنصار  | حديث زيد بن ثابت عن النبي(ص) : ( 21654، 21578).


- ﺗﻌﻠﻴﻖ ﺷﻌﻴﺐ ﺍﻷﺭﻧﺆﻭﻁ: ﺣﺪﻳﺚ ﺻﺤﻴﺢ ﺑﺸﻮﺍﻫﺪﻩ...).


- ﻣﺴﻨﺪ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺃﺣﻤﺪ ﺑﻦ ﺣﻨﺒﻞ ﺍﻟﻤﺆﻟﻒ: ﺃﺣﻤﺪ ﺑﻦ ﺣﻨﺒﻞ ﺃﺑﻮ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺸﻴﺒﺎﻧﻲ ﺍﻟﻨﺎﺷﺮ: ﻣﺆﺳﺴﺔ ﻗﺮﻃﺒﺔ – ﺍﻟﻘﺎﻫﺮﺓ ﻋﺪﺩ ﺍﻷﺟﺰﺍﺀ : 6 ﺍﻷﺣﺎﺩﻳﺚ ﻣﺬﻳﻠﺔ ﺑﺄﺣﻜﺎﻡ ﺷﻌﻴﺐ ﺍﻷﺭﻧﺆﻭﻁ ﻋﻠﻴﻬﺎ - ‏( 5 / 181 ‏) ﺡ 21618.


Shahararren malamnin Tafsir da Hadisi; Jalaluddeen Suyuti, ya riwaito hadisus-Sakalain da sigar Annabi(saw) yace; ya bar mana khalifofi 2: Qur'ani da Ahlul-bayt(as).


- ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ﺍﻟﺼﻐﻴﺮ ﻟﻠﺴﻴﻮﻃﻲ ﺗﺤﻘﻴﻖ ﺣﻤﺪﻱ ﺍﻟﺪﻣﺮﺩﺍﺵ ﺝ 2 ﺹ 544 ﺣﺪﻳﺚ ﺭﻗﻢ 2631 ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻤﺤﻘﻖ ‏(ﺻﺤﻴﺢ ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺃﺣﻤﺪ).


- ﻣﺴﻨﺪ ﺃﺣﻤﺪ ﺗﺤﻘﻴﻖ ﺍﺣﻤﺪ ﺷﺎﻛﺮ ﻭﺣﻤﺰﺓ ﺍﻟﺰﻳﻨﻲ ﺍﻟﻤﺠﻠﺪ 16 ﺹ 28 ﺭﻗﻢ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ 21470 ﻁ ﺩﺍﺭ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻤﺤﻘﻖ: ﺇﺳﻨﺎﺩﻩ ﺣﺴﻦ.


Wannan hadisi na As-Salakain da sigar; Annabi(saw) ya bar mana khalifofi 2: Qur'ani da Ahlul-bayt(as) mutawatiri ne:


ﺍﻟﺮﻭﺍﻳﺔ ﺻﺮﻳﺤﺔ ﻓﻲ ﺩﻻﻟﺘﻬﺎ ﻋﻠﻰ ﺧﻼﻓﺔ ﺍﻟﻌﺘﺮﺓ ﺍﻟﻄﺎﻫﺮﺓ ﻟﻠﻨﺒﻲ ﺍﻷﻋﻈﻢ ﻭﻗﺪ ﺻﺤﺤﻬﺎ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻭﺍﻹﻣﺎﻡ ﺍﻟﺴﻴﻮﻃﻲ ﻭﺍﻹﻣﺎﻡ ﺍﻟﻬﻴﺜﻤﻲ ﻭﺍﻟﻌﻼﻣﺔ ﺷﻌﻴﺐ ﺍﻷﺭﻧﺆﻭﻁ ﻭﺍﻟﻌﻼﻣﺔ ﺍﻟﺴﻤﻬﻮﺩﻱ ﻭﺍﻟﺸﻴﺦ ﺍﻟﺪﻛﺘﻮﺭ ﻭﺻﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﺤﻤﺪ ﻋﺒﺎﺱ ﻭﻣﺼﻄﻔﻰ ﺑﻦ ﺍﻟﻌﺪﻭﻱ ﻭﺍﻹﻣﺎﻡ ﺍﻟﺒﻮﺻﻴﺮﻱ ﻭ ﺍﻟﺪﻛﺘﻮﺭ ﺑﺎﺳﻢ ﺑﻦ ﻓﻴﺼﻞ ﺍﻟﺠﻮﺍﺑﺮﺓ ﻭﺧﺎﻟﺪ ﺑﻦ ﺃﺣﻤﺪ ﺑﺎﺑﻄﻴﻦ ﻭﻋﺎﺩﻝ ﺑﻦ ﻳﻮﺳﻒ ﺍﻟﻌﺰﺍﺯﻱ، ﺃﺣﻤﺪ ﺑﻦ ﻓﺮﻳﺪ ﺍﻟﻤﺰﻳﺪﻱ...


Kamar yanda Qur'ani ya rabu zuwa Juzu'i, Hizifi, Sura, Aya... Hakama khalifofin Annabi(saw) a cikin Ahlul-Bayt(as) suka rabu zuwa 12.


Bayan da Annabi Muhammad(saw) ya tabbatar mana da cewa; Qur'ani da Ahlul-Bayt(as) ne khalifofinsa; sai kuma Annabi(saw) ya tabbatar mana da cewa; khalifofinsa 12 (a cikin Ahlul-Bayt(as):


Bukhari, Muslim, Tirmizi, Abu Dawud... sun riwaito Jabir Ibn Samurah ya ce naji Annabi(saw) yana cewa: Addinin (Musulunci) zai samu daukaka (da kima); har a tashi Qiyama, matukar ku (Musulmai kun bari) khalifofi 12 sun yi jagoranci, dukkansu Quraishawa ne:


1822 ( 10 )   حَدَّثَنَا  قُتَيْبَةُ بْنُ سَعِيدٍ ،  وَأَبُو بَكْرِ بْنُ أَبِي شَيْبَةَ ، قَالَا : حَدَّثَنَا  حَاتِمٌ  - وَهُوَ : ابْنُ إِسْمَاعِيلَ - عَنِ  الْمُهَاجِرِ بْنِ مِسْمَارٍ ، عَنْ  عَامِرِ بْنِ سَعْدِ بْنِ أَبِي وَقَّاصٍ ، قَالَ :  كَتَبْتُ إِلَى  جَابِرِ بْنِ سَمُرَةَ  مَعَ غُلَامِي نَافِعٍ : أَنْ أَخْبِرْنِي بِشَيْءٍ سَمِعْتَهُ مِنْ رَسُولِ اللَّهِ(ص) قَالَ : فَكَتَبَ إِلَيَّ : سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ(ص)... يَقُولُ : "لَا يَزَالُ الدِّينُ قَائِمًا، حَتَّى تَقُومَ السَّاعَةُ، أَوْ يَكُونَ عَلَيْكُمُ اثْنَا عَشَرَ خَلِيفَةً كُلُّهُمْ مِنْ قُرَيْشٍ".


- صحيح مسلم : كتاب : الإمارة  | باب : الناس تبع لقريش ( 1821, 2305, 2919, 2923 ).


- صحيح البخاري ( 7222 ).


- سنن أبي داود ( 4279, 4280 ).


- سنن الترمذي ( 2223 ).


Ahmad Ibn Hanbal a littafinsa "Musnad"; ya riwaito wannan hadisin na khalifofi 12 da sigogi da isnadai masu ya gaske, daya daga ciki:


Daga Sha'abi, daga Masruq, ya ce; wata rana muna zaune tare da Abdullahi Ibn Mas'ud yana karantar da mu Qur'ani, sai wani mutum ya ce da shi, ya Aba Abdurrahman! shin kun taba tambayar Annabi Muhammad(saw) dangane da khalifofinsa a cikin Al-ummarsa guda nawa ne? sai Abdulahi Ibn Mas'ud ya ce: Lallai mun tambayi Annabi(saw) kan adadin khalifofinsa a bayansa sai ya ce damu: "KHALIFOFI A BAYA NA 12 NE KAMAR JERIN SHUWAGABANNI BANI ISRA'ILA":


ﺣﺪﺛﻨﺎ ﺣﺴﻦ ﺑﻦ ﻣﻮﺳﻰ ﺣﺪﺛﻨﺎ ﺣﻤﺎﺩ ﺑﻦ ﺯﻳﺪ ﻋﻦ ﺍﻟﻤﺠﺎﻟﺪ ﻋﻦ ﺍﻟﺸﻌﺒﻲ ﻋﻦ ﻣﺴﺮﻭﻕ ﻗﺎﻝ: ﻛﻨﺎ ﺟﻠﻮﺳﺎ ﻋﻨﺪ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻣﺴﻌﻮﺩ ﻭﻫﻮ ﻳﻘﺮﺋﻨﺎ ﺍﻟﻘﺮﺁﻥ ﻓﻘﺎﻝ ﻟﻪ ﺭﺟﻞ ﻳﺎ ﺃﺑﺎ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﻫﻞ ﺳﺄﻟﺘﻢ ﺭﺳﻮل الله(ص) ﻛﻢ ﺗﻤﻠﻚ ﻫﺬﻩ ﺍﻷﻣﺔ ﻣﻦ ﺧﻠﻴﻔﺔ ﻓﻘﺎﻝ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻣﺴﻌﻮﺩ ﻣﺎ ﺳﺄﻟﻨﻲ ﻋﻨﻬﺎ ﺃﺣﺪ ﻣﻨﺬ ﻗﺪﻣﺖ ﺍﻟﻌﺮﺍﻕ ﻗﺒﻠﻚ ﺛﻢ ﻗﺎﻝ ﻧﻌﻢ ﻭﻟﻘﺪ ﺳﺄﻟﻨﺎ ﺭﺳﻮﻝ ا ﻓﻘﺎﻝ ﺍﺛﻨﺎ ﻋﺸﺮ ﻛﻌﺪﺓ ﻧﻘﺒﺎﺀ ﺑﻨﻲ ﺇﺳﺮﺍﺋﻴﻞ.


- مسند أحمد (3772, 20802, 20805, 20814, 20817, 20819, 20821, 20823, 20830, 20836, 20838, 20839, 20841, 20860, 20862, 20863, 20872, 20879, 20880, 20889, 20892, 20896, 20902, 20905, 20906, 20922, 20923, 20924, 20926, 20927, 20937, 20939, 20941, 20946, 20951, 20952, 20959, 20962, 20966, 20967, 20996, 21013, 21020, 21021, 21033, 21036, 21039, 21050 ).


Hadisan ayyana Khalifofi 12 bayan Annabi(saw) ya zo a littattafan Ahlus-Sunnah masu yawan gaske, kadan daga cikinsu:


- Sawa'iqul-muhriqa, na Ibn Hajar, BABI NA 11, FASALI NA 2, j 12.


- Kanzul-ummal, na Muttaqil hindi, juzu'i na 6, shafi na 160, 13 : 27.


- Yanabi'ul mawadda, na Sulaimanul Qanduzi Al-hanafi, BABINA 77.


- An-nihaya wal bidaya, na Ibn Kasir, juzi'i na 6, shafina 249 - 250.


- Shawahidut-Tanzil, na Al-Haskani, 1 : 455, hadisi mai numba; 626.


- Mustadrak na al-Hakim, 4 : 501.


- Fathul-Bari, na Ibn Hajar Asqalani, 16:339.


- Majma al-Zawa'id, na Ali Ibn Abu Bakr al-Haythami, 5 : 190.


- Talkhis al-Mustadrak, na Al-Dhahabi, 4 : 501.


- Tarikh al-Khulafa, na Suyudi da  Jami' al-Saghir 1 : 75. Da sauransu.


Domin rufe bakin masu tawili sai Annabi(saw) ya ambaci sunayensu daya bayan daya; a jere kamar yanda yazo a littafin Fara'idus-Simdain, na Hamwiyniy As-shafi'i, Yanabi'ul-muwadda, na Sulaiman Al-Qanduzi Al-hanafi, da wasu littattafan Ahlus-Sunnah masu yawan gaske, daga Ibn Abbas(r) ya ce:


"Jundal Ibn Junadah ya zo wajen Annabi Muhammad(saw), ya ce da Annabi(saw); gayamin suwaye wasiyyiyanka (khalifofinka); don idan kayi wafati inyi riko da su. (Domin babu wani Annabi face yana da wasiyyi, wasiyyin Annabi Musa(as) shine Yusha'u bin Nun(as). Sai Annabi(saw) ya ce: "Wasiyyiyaina (khalifofina) 12 ne... : (1) Ali bin abi Talib(as); baban Imamai, bayansa (sai jikoki na) (2) Hasan(as) da (3) Husain(as), (kayi riko da su) kar ka damu; don wasu basu bisu ba. Bayan su, sai kuma Shuwagabanni 9 zasu biyo baya daga tsatson Husain(as). Sai Jundal ya ce; fada min sunayen su? Sai Annabi(saw) ya ce: "Idan Husain(as) ya wuce sai dansa (4) Ali Zainul-abideen(as), Idan Ali(as) ya wuce sai dansa (5) Muhammad Al-Bakir(as), Idan Muhammad(as) ya wuce sai dansa (6) Ja'afar As-Sadiq(as), Idan Ja'afar(as) ya wuce sai dansa (7) Musa Al-Kazim(as), Idan dansa Musa(as) ya wuce sai dansa (8) Ali Ar-Rida(as), Idan Ali (as) ya wuce sai dansa (9) Muhammad Al-Jawad(as), Idan Muhammad(as) ya wuce sai dansa (10) Ali Al-Hadi(as), Idan Ali(as) ya wuce sai dansa (10) Hasan Al-Askari(as), idan Hasan(as) ya wuce sai dansa (12) (Muhammad(as) Al-mahdi(as); wanda akewa lakabi da Al-Qa'im, Al-hujjah, zai yi Gaiba (fakuwa bayan an haifeshi), sannan ya bayyana; don ya cika Duniya da adalci, bayan ta cika da barna da zalunci":


ﻭﺭﻭﻯ ﻓﻲ ﻳﻨﺎﺑﻴﻊ ﺍﻟﻤﻮﺩﺓ ﻋﻦ ﺍﻟﻤﻨﺎﻗﺐ ﻟﻠﺨﻮﺍﺭﺯﻣﻲ ﺭﻭﺍﻳﺔ ﺍﺧﺮﻯ ﺭﻭﺍﻫﺎ ﺟﺎﺑﺮ ﺑﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻷﻧﺼﺎﺭﻱ ﻗﺎﻝ: ﺩﺧﻞ ﺟﻨﺪﻝ ﺑﻦ ﺟﻨﺎﺩﺓ... ﻋﻠﻰ ﺭﺳﻮﻝ الله(ص) ﻓﻘﺎﻝ: ....ﺃﺧﺒﺮﻧﻲ ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ(ص) ﻋﻦ ﺃﻭﺻﻴﺎﺋﻚ ﻣﻦ ﺑﻌﺪﻙ ﻷﺗﻤﺴّﻚ ﺑﻬﻢ. ﻗﺎﻝ: ﺃﻭﺻﻴﺎﺋﻲ ﺍﻹﺛﻨﻰ ﻋﺸﺮ. ﻗﺎﻝ ﺟﻨﺪﻝ: ﻫﻜﺬﺍ ﻭﺟﺪﺗﻬﻢ ﻓﻲ ﺍﻟﺘﻮﺍﺭﺓ. ﻭﻗﺎﻝ: ﺳﻤّﻬﻢ ﻟﻲ ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ(ص). ﻓﻘﺎﻝ : ﺃﻭّﻟﻬﻢ ﺳﻴّﺪ ﺍﻷﻭﺻﻴﺎﺀ ﺃﺑﻮ ﺍﻷﺋﻤّﺔ ﻋﻠﻲ، ﺛﻢّ ﺍﺑﻨﺎﻩ ﺍﻟﺤﺴﻦ ﻭﺍﻟﺤﺴﻴﻦ ﻓﺎﺳﺘﻤﺴﻚ ﺑﻬﻢ ﻭﻻ ﻳﻐﺮﻧّﻚ ﺟﻬﻞ ﺍﻟﺠﺎﻫﻠﻴﻦ، ﺛﻢّ ﻗﺎﻝ: ﻓﺈﺫﺍ ﺍﻧﻘﻀﺖ ﻣﺪّﺓ ﺍﻟﺤﺴﻴﻦ ﻓﺎﻹﻣﺎﻡ ﺍﺑﻨﻪ ﻋﻠﻲ ﻭﻳﻠﻘّﺐ ﺑﺰﻳﻦ ﺍﻟﻌﺎﺑﺪﻳﻦ، ﻓﺒﻌﺪﻩ ﺍﺑﻨﻪ ﻣﺤﻤّﺪ ﻳﻠﻘّﺐ ﺑﺎﻟﺒﺎﻗﺮ، ﻓﺒﻌﺪﻩ ﺍﺑﻨﻪ ﺟﻌﻔﺮ ﻳﺪﻋﻰ ﺑﺎﻟﺼﺎﺩﻕ، ﻓﺒﻌﺪﻩ ﺍﺑﻨﻪ ﻣﻮﺳﻰ ﻳﺪﻋﻰ ﺑﺎﻟﻜﺎﻇﻢ، ﻓﺒﻌﺪﻩ ﺍﺑﻨﻪ ﻋﻠﻲ ﻳﺪﻋﻰ ﺑﺎﻟﺮﺿﺎ، ﻓﺒﻌﺪﻩ ﺍﺑﻨﻪ ﻣﺤﻤّﺪ ﻳﺪﻋﻰ ﺑﺎﻟﺘﻘﻲ ﻭﺍﻟﺰﻛﻲ، ﻓﺒﻌﺪﻩ ﺍﺑﻨﻪ ﻋﻠﻲ ﻳﺪﻋﻰ ﺑﺎﻟﻨﻘﻲ ﻭﺍﻟﻬﺎﺩﻱ، ﻓﺒﻌﺪﻩ ﺍﺑﻨﻪ ﺍﻟﺤﺴﻦ ﻳﺪﻋﻰ ﺑﺎﻟﻌﺴﻜﺮﻱ، ﻓﺒﻌﺪﻩ ﺍﺑﻨﻪ ﻣﺤﻤّﺪ ﻳﺪﻋﻰ ﺑﺎﻟﻤﻬﺪﻱ ﻭﺍﻟﻘﺎﺋﻢ ﻭﺍﻟﺤﺠّﺔ، ﻓﻴﻐﻴﺐ ﺛﻢّ ﻳﺨﺮﺝ، ﻓﺈﺫﺍ ﺧﺮﺝ ﻳﻤﻸ ﺍﻷﺭﺽ ﻗﺴﻄﺎً ﻭﻋﺪﻻً ﻛﻤﺎ ﻣﻠﺌﺖ ﺟﻮﺭﺍً ﻭﻇﻠﻤﺎً.


Doriya akan cewa; Annabi Muhammad(saw) ya ce; "Dana Husain(as) Imami (shugaba) ne, dan Imami (Shugaba), dan uwan Imami (Shugaba), baban Imamai (shuwagabanni) 9:


ﻋﻦ ﺍﻟﻨﺒﻲ(ص) ﺍﻧّﻪ ﻗﺎﻝ: ﺍﻥّ ﺍﺑﻨﻲ ﻫﺬﺍ ـ ﻳﻌﻨﻲ ﺍﻟﺤﺴﻴﻦ(ع) ـ ﺇﻣﺎﻡ ﺍﺑﻦ ﺇﻣﺎﻡ ﺃﺧﻮ ﺇﻣﺎﻡ ﺃﺑﻮ ﺃﺋﻤّﺔ ﺗﺴﻌﺔ ﺗﺎﺳﻌﻬﻢ ﻗﺎﺋﻤﻬﻢ.


ﻋﻦ ﺳﻠﻤﺎﻥ ﺍﻟﻔﺎﺭﺳﻲ ﺃﻧّﻪ ﻗﺎﻝ: ﺩﺧﻠﺖ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻨّﺒﻲ ‏(ﺹ)، ﻓﺈﺫﺍ ﺍﻟﺤُﺴﻴﻦ ﻋﻠﻰ ﻓﺨﺬﻩ ﻭﻫﻮ ﻳﻘﺒّﻞ ﻋﻴﻨﻴﻪ ﻭﻳﻠﺜﻢ ﻓﺎﻩ ﻭﻫﻮ ﻳﻘﻮﻝ: ﺃﻧﺖ ﺳﻴّﺪ ﺍﺑﻦ ﺍﻟﺴﻴّﺪ، ﺃﻧﺖ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺍﺑﻦ ﺍﻹﻣﺎﻡ، ﺃﻧﺖ ﺣﺠّﺔ ﺍﺑﻦ ﺍﻟﺤﺠّﺔ ﺃﺑﻮ ﺍﻟﺤﺠﺞ ﺍﻟﺘﺴﻌﺔ ﻣﻦ ﺻﻠﺒﻚ ﺗﺎﺳﻌﻬﻢ ﻗﺎﺋﻤﻬﻢ.


ﺭﻭﻯ ﺍﻟﺨﻮﺍﺭﺯﻣﻲ ﺑﺎﺳﻨﺎﺩﻩ ﻋﻦ ﺳﻠﻤﺎﻥ ﺍﻟﻤﺤﻤّﺪﻱ، ﻗﺎﻝ: ﺩﺧﻠﺖ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻨﺒﻲ(ص)، ﻭﺇﺫﺍ ﺍﻟﺤﺴﻴﻦ ﻋﻠﻰ ﻓﺨﺬﻩ ﻭﻫﻮ ﻳﻘﺒّﻞ ﻋﻴﻨﻴﻪ ﻭﻳﻠﺜﻢ ﻓﺎﻩ ﻭﻳﻘﻮﻝ : ﺍﻧﻚ ﺳﻴﺪ ﺍﺑﻦ ﺳﻴﺪ ﺃﺑﻮ ﺳﺎﺩﺓ . ﺍﻧﻚ ﺇﻣﺎﻡ، ﺍﺑﻦ ﺇﻣﺎﻡ، ﺃﺑﻮ ﺃﺋﻤﺔ . ﺍﻧﻚ ﺣﺠﺔ ﺍﺑﻦ ﺣﺠﺔ ﺃﺑﻮ ﺣﺠﺞ ﺗﺴﻌﺔ، ﻣﻦ ﺻﻠﺒﻚ ﺗﺎﺳﻌﻬﻢ ﻗﺎﺋﻤﻬﻢ)


ﺃﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ(ص)، ﻗﺎﻝ ﻟﺴﺒﻄﻪ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺍﻟﺤﺴﻴﻦ: ﺍﺑﻨﻲ ﻫﺬﺍ ﺇﻣﺎﻡ، ﺍﺑﻦ ﺇﻣﺎﻡ، ﺃﺧﻮ ﺇﻣﺎﻡ، ﺃﺑﻮ ﺃﺋﻤﺔ ﺗﺴﻌﺔ، ﺗﺎﺳﻌﻬﻢ ﻗﺎﺋﻤﻬﻢ...


Wadanan hadisan sun zo a littafan Ahlus-Sunnah masu yawan gaske, kadan daga ciki:


- ﻛﻨﺰ ﺍﻟﻌﻤّﺎﻝ ﺝ 12 ﺹ 125 ﺍﻟﺮﻗﻢ 34312 ﻃﺒﻊ ﺣﻠﺐ .


- ﺍﻟﻬﻴﺜﻤﻲ : ﻣﺠﻤﻊ ﺍﻟﺰﻭﺍﺋﺪ ﺝ 9 ﺹ .185


‏- ﻣﻘﺘﻞ ﺍﻟﺤﺴﻴﻦ ﺝ 1 ﺹ .146


‏- ﺗﺎﺭﻳﺦ ﺑﻐﺪﺍﺩ ﺝ 2 ﺹ .204


‏- ﺍﻟﻤﺤﺐ ﺍﻟﻄﺒﺮﻱ : ﺫﺧﺎﺋﺮ ﺍﻟﻌﻘﺒﻰ ﺹ 136، 133...

 ‏(ﻁ 1356 ﻫـ‏) .


‏- ﺍﺑﻦ ﻋﺴﺎﻛﺮ : ﺗﺮﺟﻤﺔ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺍﻟﺤﺴﻴﻦ ﻣﻦ ﺗﺎﺭﻳﺦ ﻣﺪﻳﻨﺔ ﺩﻣﺸﻖ ﺹ 135 ﺭﻗﻢ 173، ﺹ 109 ﺭﻗﻢ 147.


- ﻛﻔﺎﻳﺔ ﺍﻟﻄﺎﻟﺐ ﺹ 420...


‏- ‏ﺍﻟﺤﻠﻲ : ﺷﺮﺡ ﺍﻟﺘﺠﺮﻳﺪ ﺹ 250 ‏( ﻃﺒﻌﺔ ﺍﻟﻌﺮﻓﺎﻥ ‏) .


‏- ﻳﻨﺎﺑﻴﻊ ﺍﻟﻤﻮﺩﺓ، باب 77...


‏- ﺍﻟﺤﻀﺮﻣﻲ : ﻭﺳﻴﻠﺔ ﺍﻟﻤﺂﻝ ﺹ 364 ﺑﺄﺳﻨﺎﺩ ﻣﺨﺘﻠﻔﺔ.


DORIYA AKAN CEWA; AYOYIN QUR'ANI DA INGANNTATTUN HADISAI MASU YAWAN GASKE SUN TABBATAR MANA IMAMAN SHIA 12 SUNE KHALIFOFIN ANNABI MUHAMMAD(SAW), MISALI, AYAR WILAYA (Q: 5 : 55), AYAR MUWADDA (Q : 42 :23), AYAR TABLIGH (Q: 4 : 59), AYAR IKMALUD-DEEN (Q: 4 : 59), AYAR ULIL-AMRI / ITA'A (Q : 4 : 59), AYAR-TAD'HIR (Q: 33 : 33), AYAR KHAIRUL-BARIYYA (Q : 99 :7-8), AYAR MUBAHALAH (Q : 3 : 61)... HADISIN GHADEER, HADISIN KISA'I, HADISIN MANZILA, HADISIN RAYA (TUTA), HADISIN DAYR, HADISIN BABUL-ILMI, HADISIN SAFINA...


Idan Annabi Muhammad(saw) bayyi wasiya da wanda zai gaje shi ba; me ya sa khalifa Abubakar yayi wasiya da Umar? Kenan Abubakar ya sabawa Sunnar Annabi(saw)?


Idan har Annabi(saw) ya ayyana khalifofi 4 a matsayin Khulafa'ur-rashidin; me ya sa akayi dimokradiyyar magudi a Sakifa?


Me ya sa Sahabbai suka taru a Sakifa don zaben khalifa? Kenan duk Sahabban da suka taru a Sakifa Jahilai ne basu san Annabi(saw) ya ayyana Abubakar a matsayin magajinsa ba? 


Kenan Abubakar da Umar basu san Annabi(saw) ayyana su a matsayin khalifofi ba? Tunda har suke musayar Khalifancin tsakanin Abu Ubaida da Abubakar? 


Me ya sa 'yar Annabi Muhammad(saw); Fatimah(as), har ta yi wafati batayiwa Abubakar mubaya'a? 


Me ya sa mafi yawan malaman Ahlus-Sunnah suka ce; Annabi(saw) bai fadi wanda zai gaje shi ba? Kenan mafi yawan jamhurin malaman Ahlus-Sunnah jahilai ne? Ko dai basu yarda da ingancin hadisan khalifancin Abubakar ba ne? 


Idan Umar ya san Annabi(saw) ya ayyana Usman; me zai sa sai ta hanyar shura za'a zabi Usman? Kenan Umar da yan kwamitin shurar sun jahilci ayyanawar Annabi(saw)? 


Me ya sa Ummul-mu'umin Aisha ta harzuka Sahabbai akan ayiwa khalifa Usman tawaye? Kenan Ummul-Mu'uminin Aisha bata san Annabi(saw) ya ayyana Usman a matsayin khalifa ba? Ina makomar Sahabban da suka kashe Usman? 


Me ya sa Ummul-Mu'uminin Aisha, Mu'awiya... suka yiwa Imam Ali(as) tawaye? Menene makomar wanda ya yaki daya daga cikin khulafa'ur-Rashidin? 


Idan har Annabi(saw) ya ayyana shekaru 30 a matsayin shekarun khalifanci a bayansa; kenan Mu'awiya da khalifofin da suka biyo bayansa ba khalifofin Annabi(saw) ba ne? Kenan duk khalifan da baya cikin khulafa'ur-Rashidin (khalifofi shiryayyu) to ba shiryayye ne ba (gairu rashid ne)?


Ina makomar hadisin khalifofi 12 a bayan Annabi(saw)? Ko bai inganta ba ne? Ko dai kuna so kuce; Annabi(saw) yayi maganar da akasinta ya faru? 


Duk Duniya akwai wata jama'a mai khalifofi 12 banda Shi'a Imamiyya?


Ya Allah ka barmu da Imaman Shia 12; Duniya da Lahira! Ka karbi ayukanmu!! Ka biya mana bukatunmu; albarkacinsu(as)!!!


Sani Muh'd Sani Muh'd

Baban humaid Mnnu//Ng0027

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post