DAGA KALAMAN HIKIMA NA IMAM ALI (A. S) !!!
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
ILLAR YIN SHAWARI DA MATA
Kamar yadda kowa ya sani ne cewa su mata suna da rauni (weak) ta kowanne bangare in dai an karantata su da maza, shi yasa ma Allah ya fifita jinsin maza a kansu ta wasu bangarori da dama.
Abinda kawai ba a fifita bangaren maza a kansu ba shine bangaren taqawa, domin da yawa ana samun mata wadanda suka fi maza taqawa. Shi yasa ma Allah (T) yake cewa :
" ABIN SANIN MAFIFICIN CIKINKU A WAJEN ALLAH SHINE MAFI TAQAWAR CIKINKU. "
Imam Ali (A. S) na cewa :
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
قال الإمام علي بن أبي طالب(ع):
" إِيَّاكَ وَمُشَاوَرَةَ النِّسَاءِ فَإِنَّ رَأْيَهُنَّ إِلَى أَفْنٍ وَعَزْمَهُنَّ إِلَى وَهْنٍ وَاكْفُفْ عَلَيْهِنَّ مِنْ أَبْصَارِهِنَّ فَحِجَابُكَ لَهُنَّ خَيْرٌ مِنَ الِارْتِيَابِ بِهِنَّ وَلَيْسَ خُرُوجُهُنَّ بِشَرٍّ مِنْ إِدْخَالِكَ مَنْ لَا يُوثَقُ [لَا تَثِقُ] بِهِ عَلَيْهِنَّ وَإِنِ اسْتَطَعْتَ أَنْ لَا يَعْرِفْنَ [يعرفهن] غَيْرَكَ فَافْعَلْ.'
" NA HANEKA GAME DA YIN SHAWARA DA MATA, DOMIN RA'AYINSU MAI RAUNI NE, KUMA HIMMARSU GAJERIYA CE. (saboda haka) KA FAKU GARE SU DAGA GANINSU, KUMA FAKUWARKA GARE SU YA FI ALKHAIRI DAGA BAYYANARKA GARE SU (yayin yin wani shawari naka).
KUMA SHARRIN FITARSU WAJE (cikin maza) BAI KAI SHARRIN SHIGOWARKA DA WANI WANDA BA KA DA YAQINI (tabbacin amincinsa) A KANSU . IDAN HAR KANA DA IKON HANA WANI YA SANSU KOMA-BAYANKA, TO, KA AIKATA. "
المصدر : غرر الحكم ودرر الكلم
Idan mutum zaiyi nazari sosai zai iya gano matsalar yin shawari da mata, domin in yana yin tabbas zai ga watarana yana da-na-sanin yin wannan shawari dasu.
Sannan hadisin na karantar damu cewa sharrin fitar mace bai kai sharrin shigowar maza mararsa aminci cikin gida ba, domin ai fitar mace ba haramun bace matuqar tana kare mutuncin kanta.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.
(08137925034)
28th July, 2024/ 21st Muharram, 1445.