AZUMI KO JUYAYI ???
Sunce : Ƴan Shi'a ku dena kuka da juyayin tuna abun da ya faru sama da shekara 1384 domin abune da ya shafi al'ummar da ta gabata , shi kuma Allah yace :
تِلْكَ أُمَّةٌ قَدْ خَلَتْ لَهَا مَا كَسَبَتْ وَلَكُمْ مَا كَسَبْتُمْ
Mu kuma muce : to kuma ku dena yin Azumin Tasu'a da Ashura saboda murnar kuɓutar Annabi Musa (a.s) da tseratar da Banu Isra'ila , suma al'ummar da suka gabata ne :
تِلْكَ أُمَّةٌ قَدْ خَلَتْ لَهَا مَا كَسَبَتْ وَلَكُمْ مَا كَسَبْتُمْ
Kuma wannan Ayar sam ba tana magana akan tunawa ko yanke alaƙa da al'umatana da ta gabata ne , Yahudawa Allah yakewa raddi saboda yanda suke ganin sune zaɓaɓɓeun Allah kowa banza ne in basu ba kuma aikin iyayensu ya wadace su , ga wanda ya koma Tafsirai da siyaƙin Alƙur'ani zai fahimci hakan .
Indai mutum yace wai kashe Imam Hussain (a.s) da abinda yafaru a tarihi ba buƙatar bincika shi saboda ya shafi al'ummar bayanmu ne , to dole ya bar karanta Alkur'ani da bin koyarwarsa domin Alƙur'ani cike yake da labaran mutan farko da jona rayuwar al'ummar Annabi Muhammad (saww) da al'umatan da suka gabata tun daga Annabi Adamu (a.s) har zuwa akan Annabi Isa (a.s) , ba don komai ba sai don mu ɗauki darasi da Izina cikin labaransu mu shiriya , shi yasa Alƙur'ani cike yake da ambaton labaran mutanen kirki da mutanen banza da masu adalci da azzalumai, ba don komai ba sai dan mu ɗauki darasi daga rayuwar adalai mu barranta daga rayuwar azzalumai , kuma wannan shine Addinin baki ɗaya .
Shine abinda yan Shi'a suke yi wajen tunawa da waƙi'ar Karbala ta wata fuskar , don su raya ambaton gaskiya su kuma ƙauracewa karya da ɓarna da ɓata , kuma abune tabbatacce duk al'ummar da basu damu da tarihin jiyansu ba yau ɗinsu ba za tayi kyau ba ballantana gobensu .
Uwa uba kuma Hadisai ingantattu , Lafiyayyu sun tabbata cewa Annabi (saww) yayi kuma da baƙin ciki ba sau ɗaya ba ba sau biyu akan kashe Imam Hussain (a.s) tun kafin waƙi'ar Karbala da shekaru kusan Sittin , kuma tabbas da yana nan zai cigaba da da yin kukan juyayin kisansa har abada , sannan dama zance da shiru da aikin Annabi saww sune Sunnah don haka Shi'a Sunnah suke yi , in kunce Azumin Tasu'a da Ashura Sunnah ce to kuka da juyayin kashe Imam Hussain (a.s) Sunnah ce , bal ma ita tafi karfi da tabbata domin batun Azumi da cika ciki akwai magana akansu ga duk wanda yayi bincike na ilmi da adalci .
Kuma ga yadda ake dangantawa Annabi (saww) koyo da yahudawa akan batun Azumi.
✍️ Khadimu A'atabi Ali Muhammad Al-Abdul Faneey Al-kanaweey
Al-muharramul Haram /1444H - 26 / 7 / 2023M