ANA BARAZANAR YIWA MATAR NATANYAHU FYADE DA KASHE WASU MANYAN JAMI'AI,



 ANA BARAZANAR YIWA MATAR NATANYAHU FYADE DA KASHE WASU MANYAN JAMI'AI,

Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar tatsuniya ya yi furuci da cewa: Ana barazanar yin fyade ga matarsa a matsayin ramakon gayya kansa,


Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar tatsuniya Benjamin Netanyahu ya bayyana fargabar bullar kashe-kashen gilla a haramtacciyar kasar tatsuniya, yana mai cewa ana kokarin tayar da tarzoma a cikin haramtacciyar kasar tatsuniya musamman tun bayan yunkurin hallaka tsohon shugaban Amurka Donald Trump a lokacin da yake jawabi a wani taron yakin neman zabe a lokacin gangami magoya bayansa.


A wata hira da ya yi da gidan talabijin na 14 na haramtacciyar kasar tatsuniya Netanyahu ya ce: Akwai makircin da akekullawa na tunzura jama’a domin gudanar da kashe-kashen gilla kan zababbun jami’ai a haramtacciyar kasar tatsuniya, kuma hakan na iya kaiwa ga fira minista da iyalansa, yana mai jaddada cewa yana fuskantar barazana ba dare ba rana. kuma akwai wadanda suke yi masa kururuwa cewa shi maci amana ne kuma mai kisan kai ne.


Ya ci gaba da cewa: Ba shi kadai ba, barazanar ta hada da iyalinsa, Yana mai zargin bangarorin ‘yan adawa da hannu a rurata wutar rikici a haramtacciyar kasar tatsuniya.


Yana mai jaddada cewa: Matarsa ​​Sarah tana fuskantar barazanar fyade da cin mutunci, da zage-zage ba dare ba rana daga iyalan yahudawa da ‘yan uwansu suka halaka da wadanda ‘yan uwansu suke hannun Falasdina a matsayin fursunonin yaki a Gaza.

@Ma'asumah Nigerian News update

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post