AN CIGABA DA ZANGA-ZANGA A KASAR BANGLADESH AL'UMMA SUN SAKE FITOWA


 


AN CIGABA DA ZANGA-ZANGA A KASAR BANGLADESH AL'UMMA SUN SAKE FITOWA


Hukumomi a kasar Bangladesh sun kafa dokar hana fita a babban birnin kasar Daka, saboda kawo karshen zanga zangar da aka dauki kwanaki ana gudanarwa a kasar.


Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kafafen yada labaran kasar Bangladesh na cewa a cikin yan kwanakin da suka gabata rikicin da ake yi ya kai ga an fasa wani gidan yari a babban birnin kasar wanda ya kai ga tserewar fursinoni da dama. Banda haka rikicin ya lakube rayukan mutane akalla 67 ya zuwa yanzu.


Labarin ya kara da cewa rikicin ya tashi ne sanadiyyar dokan da gwamnatin kasar ta kafa wacce ta ware mukamai masu muhimmanci a kasar don dangin shugaban daya jagoranci kasar zuwa yencin kai a shekara 1971.


Kakakin gwamnatin kasar Naeemul Islam Khan ya bayyana cewa zasu tura sojoji don dawo da zama lafiyan a Ƙasar musamman a birnin Dakar.


@Ma'asumah Nigerian News update

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post