AN BUDEWA TSOHON SHUGABAN ƘASAR AMURKA TRUMP WUTA A WAJAN YAKIN NEMAN ZABE...
Bayanai daga Amurka na cewa mutum biyu sun mutu, lokacin da wani dan bindiga ya bude wuta a wurin yakin neman zaben tsohon shugaban kasar Donald Trump Jaridar Washington Post, ta ce cikin mutanen har da maharinda ya kai harin.
Hotunan da aka watsa a Internet sun nuna lokacin da Donald Trump ya sunkuya cikin gaggawa ya buya a karkashin abun magana, yayin da yake tsaka da jawabi a kan duro. Nan da nan jami'an tsaro na yan sanda da wadanda ke ba shi kariya suka kewaye shi suka yi masa rumfa, daga bisani suka fice da shi a gaggauce.
An fita da shi yana takawa dakyar, jini na zuba a kunnensa da fuskarsa magoya bayansa sun rika yarda allunan goyon bayansa suna ranta a na kare, wasu na kwantawa a kasa don kare kansu, Cikin yan mintuna kalilan wurin ya watse baki daya. A cikin wata sanarwa da hukumar kare fararen hula ta kasar ta fitar, ta ce Trump na cikin koshin lafiya kuma an kare rayuwarsa. Sanarwar ta kara da cewa yanzu haka ana gudanar da bincike mai zurfi kuma za a fitar da karin bayani idan an samu.
Shugaba Biden ya bayyana a gaban manema labarai a mahaifarsa ta Delaware, inda yayi Allah wadai da harin, yana cewa zai yi magana da abokin hamayyar na sa, domin taya shi alhini. Tuni suma yan siyasa daga jam'iyyar tsohon shugaban kasar Trump ta Republican har ma da abokan hamayyarsa na Democrats suka fara yin tir da harin, suna kuma addu'ar samun sauki da nuna goyon baya ga tsohon shugaban.
Cikin dakiku kadan da faruwar wannan lamari shafukan sada zumunta sun cika makil da jita-jita da labaran kanzon kuregen da ba su da tabbas. A shafin X wanda a baya aka fi sani da twitter, kalmar "staged" watau ‘’Kitsa abu’’ ta fara wadari, inda galibi abokan adawar Trump ke zargin kitsa wannan al’amari aka yi domin a karfafa damarsa ta samun nasara a zaben watan Nuwamba ta hanyar sanya tausayinsa a zukatan masu kada kuri’a.
A sani, babu wata shaida da ke tabbatar da wannan ikirari. A gefe guda kuma wasu magoya bayan Mista Trump na yada cewa faruwar wannan al’amari ya kara tabbatar da zargin da suka jima suna yi ta cewa akwai wasu mamugunta masu rike da iko, da ke neman rayuwarsa. Shima dai wannan zargi ne mara tushe ballantana makama, domin babu wata hujja da ta nuna hakan. Dama dai a duk sa’ad da aka samu faruwar wani lamari irin wannan labaran kanzon kurege na yaduwa kamar wutar daji,sai dai a kula, yawanci babu gaskiya a cikinsu.
@Ma'asumah Nigerian News update