AKALLA FALASDINAWA 6,400 NE SUKA BACE A ZIRIN GAZA TUBAYAN BULLAR YAKI



AKALLA FALASDINAWA 6,400 NE SUKA BACE A ZIRIN GAZA TUBAYAN BULLAR YAKI

Kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta sanar da cewa: Falasdinawa 6,400 ne suka bace a Gaza tun daga farkon fara kai hare-hare kjan yankin


Kungiyar ba da agaji ta kasa da kasa Red Cross ta sanar da cewa: Falasdinawa kusan 6,400 ne a Gaza suka shiga cikin wadanda aka tabbatar da bacewarsu, tana mai bayanin cewa; Mafi yawansu suna karkashin baraguzan gine-gine ko wadanda ake tsare da su a gidajen yarin gwamnatin  HKI ko kuma an kashe su tare da binne gawawwakinsu ba tare da tantance ko su wane ne ba, a daidai lokacin da aka kasa samun hanyar sadarwa tsakanin wasu mutane da dama da iyalansu saboda hare-haren wuce gona da iri da ake ci gaba da kai kan yankin.


Kungiyar ta Red Cross ta kara da cewa: An rubuta wasu sabbin sunayen wadanda suka bace da suka kai Falasdinawa 1,100, tana mai bayyana cewa har yanzu ba a warware wannan matsalar ba tun daga watan Afrilun wannan shekara.


Tun bayan da aka fara yakin Zirin Gaza, kungiyar agaji ta Red Cross ta bada rahoton cewa akwai Falasdinawa sama da 8,700 da suka bata a yankin, kuma ta hada kai da iyalai Falasdinawa 7,429 wajen tattara bayanai kan batun.


A cikin wannan mahallin, Sarah Davies, mai magana da yawun kungiyar Red Cross ta kasa da kasa, ta yi nuni da cewa: Kwamitin da kungiyar Red Cross ya nada kan batun, yana karbar kiran mutane  tsakanin 500 zuwa 2,500 a kan layukan wayarsa a mako-mako, tare da bayyana cewa galibin wadannan suke kiraye-kirayen suna da alaka da bacewar ‘yan uwa.

@ma'asumah Nigerian News update

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post