Harkar musulunci ƙarƙashin Jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) tayi gangamin tinawa da Imam Khomaini (QS) a babban masallacin juma'a na ƙasa dake Abuja.
A Juma'a harkar musulunci ƙarƙashin Jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), ta fara gabatar da tarurruka domin tinawa da gwarzon mujahidi Imam Khomaini (QS), taron wanda aka far yau Juma'a da gangamin tinawa da shi a masallacin ƙasa dake Abuja.
Yayin gangamin almajiran Shaikh Zakzaky (H) sun la'anci haramtacciyar ƙasar Isra'ila da Amurka tare da nuna goyon baya ga al'ummar ƙasar Falasdinu. Ga rahoton gangamin cikin hotuna.
Tags:
Harkar Musulunci